Tinubu Ya Naɗa Madadin Garba Shehu Da Wasu Muƙaman Da Dama

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tshohon Babban Manaja kuma Editan Jaridar Leadership, Kingsley Stanley Nkwocha, a matsayin Babban Mai Temakawa Shugaban Ƙasa, SSA a ɓangaren Kafafen Yaɗa Labarai da Sadarwa.

Shugaban ya naɗa Nkwocha ne tare da wasu da za su yi aiki a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Waɗanda Tinubun ya naɗa domin yin aiki a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasar sun haɗa da Tope Fasua a matsayin Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Tattalin Arziƙi a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Naɗa Jamila Da Ayodele A Matsayin Ministocin Matasa

Sauran naɗe-naɗen na ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasar sun haɗa da Sadiq S Jambo a matsayin Mai Bayar da Shawara kan Tattalin Arziƙi; Dr. Muhammad Bulama a matsayin Babban Mai Temakawa kan Aiyuka na Musamman; Mahmud Muhammad, Mai Temakawa na Musamman kan Harkokin Gida a Arewa Maso Gabas; da kuma Ahmed Ningi a matsayin Babban Mai Temakawa kan Kafafen Sadarwa na Zamani da Kai wa Ɗaukin Gaggawa.

Haka kuma Shugaban Ƙasar ya naɗa marubuci a jaridu kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Gimba Kakanda a matsayin Babban Mai Temakawa kan Harkokin Bincike da Bayar da Bayanai a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Bola Ahmed Tinubu
Comments (0)
Add Comment