Tinubu Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Cigaban Tattalin Arziƙin Najeriya, Ya Buƙaci A Cigaba Da Haƙuri

Shugaba Bola Tinubu ya nuna farin cikinsa kan ƙaruwar tattalin arziƙin Najeriya da ya kai kashi 3.46% a ƙarshen kwata ta uku ta 2024, yana mai danganta hakan da gyare-gyaren tattalin arziƙi da gwamnatinsa ta yi, amma ya ce akwai bukatar ƙarin matakai don inganta rayuwar al’umma. 

A wata sanarwa da Mai Bada Shawara na Musamman Sunday Dare ya fitar, Tinubu ya ce yana farin ciki da rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS). 

“Ba za mu huta ba sai mun tabbatar da cewa ƴan Najeriya sun ji daɗin wannan cigaba a rayuwarsu,” in ji shugaban. 

Rahoton ya nuna cigaban da aka samu a bangarori irin su noma, sufuri, fasahar sadarwa, da masana’antu, inda noma ya ba da gudummawar kashi 28.65% ga tattalin arziƙi na GDP. 

Gyare-gyaren da za ai sun haɗa da shirye-shiryen rage haraji da sauye-sauyen tattalin arziƙi don rage nauyin da ke kan ƙananan ƴan kasuwa da haɓaka halayyar gudanar da adalci. 

Tinubu ya sake jadadda ƙudurinsa na cimma tattalin arziƙin da zai kai dala tiriliyan 1 nan da shekarar 2030, yana mai cewa, “Wannan cigaba wata dama ce, amma muna kan hanya zuwa rabon arziƙi ga kowa.”

Comments (0)
Add Comment