Tinubu Ya Rage Farashin Wankin Ƙoda A Asibitocin Gwamnatin Tarayya

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da rage farashin jinyar dialysis wato wankin ƙoda a asibitocin gwamnatin tarayya daga ₦50,000 zuwa ₦12,000 a kowanne yi ɗaya, matakin da gwamnati ta ce zai kawo sauƙi ga dubban marasa lafiya.

Ɗan taƙaitaccen bayani daga Mai Ba da Shawara ga Shugaban Ƙasa kan Manufofi, Daniel Bwala, a X ya ce, “Tare da wannan mataki, an rage farashin kowanne zaman dialysis daga ₦50,000 zuwa ₦12,000, wanda zai kawo sauƙi ga dubban ƴan ƙasa masu fama da cututtukan ƙoda”.

An fara aiwatar da wannan tallafin a manyan asibitocin tarayya a kowane yanki na ƙasa, ciki har da FMC Ebute-Metta (Lagos), FMC Jabi (Abuja), UCH Ibadan, FMC Owerri, UMTH Maiduguri, FMC Abeokuta, LUTH Lagos, FMC Azare, UBTH Benin da UCTH Calabar.

Bwala ya bayyana cewa za a ƙara wasu cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya kafin ƙarshen shekara don faɗaɗa damar samun wannan rangwame, tare da tunatar da cewa Tinubu ya kuma amince da C-sections kyauta don mata masu juna biyu a asibitocin tarayya.

A cewarsa, “Waɗannan matakai suna nuna Ajandar ‘Renewed Hope’ ta Shugaban wajen tabbatar da cewa babu wani ɗan Najeriya da za a hana samun kulawar lafiya saboda tsada”, matakin da ake sa ran zai rage mace-macen da za a iya kaucewa.

Masu ruwa da tsaki a fannin lafiya sun nuna maraba da wannan tsari amma sun nuna buƙatar tsaurara sanya ido kan ingancin aiwatarwa da wadatar kayan aiki.

Idan gwamnati ta ci gaba da faɗaɗa tsarin zuwa ƙarin asibitoci da tabbatar da kayan aiki, za a samu sauƙi mai ma’ana ga marasa lafiya, musamman a yankuna masu nisa.

Comments (0)
Add Comment