Tinubu Ya Sanya Sharaɗi Kafin A Ƙara Kuɗin Shan Lantarki A Najeriya

Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyana cewar, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya matsa lamba kan cewar dole ne ƙasa ta cimma ƙaruwar wadatar hasken lantarki kafin ta ƙara kuɗin shan lantarkin a kan ƴan ƙasa.

Ya ce, Tinubu ya dakatar da aiwatar da ƙarin kuɗin shan lantarki tare da jaddada cewar akwai buƙatar a sanya tallafi a shan wutar lantarki a faɗin ƙasa.

Adelabu na wannan magana ne a taron manema labarai da ya shirya jiya Laraba a Abuja kan biyan kuɗin lantarki wanda zai jawo ƙaruwar lantarki a ƙasa.

Ya ƙara da cewa, tun watannin baya ya kamata a ƙara kuɗin shan lantarki a Najeriya amma shugaban ƙasa ya ce, matuƙar ba a ƙara yawan wutar da ƴan Najeriya ke amfani da ita ba to ba za a canja farashin wutar ba.

Bola Ahmed Tinubu
Comments (0)
Add Comment