Gwamnatin Tarayya ta ce, duk da kasancewar hukuncin ranar Alhamis da ya tabbatar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, shugaban a shirye yake ya yi aiki da abokan takararsa a zaɓen 25 ga watan Fabarairu, wato Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na Jam’iyyar Labour.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a jiya Juma’a biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar da Tinubu a matsayin wanda ya ci zaɓe tare da korar ɗaukaka ƙarar da Atiku da Obi suka yi.
Kotun Ƙoli a ranar Alhamis ta tabbatar da hukunci ranar 6 ga Satumba wanda Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Haruna Tsammani ta yi na korar ƙarar da Atiku da Obi suka shigar bisa rashin cikakkun hujjoji.
A dalilin rashin gamsuwa da hukuncin ne, ƴan takarar na jami’iyyun PDP da LP suka ɗaukaka ƙara a Kotun Ƙoli tare da buƙatar kotun ta yi watsi da hukuncin kotun baya na tabbatar da nasara ga Tinubu, ta bayyana su a matsayin waɗanda suka ci zaɓe.
Alƙalai bakwai na Kotun Ƙoli ƙarƙashin jagorancin Inyang Okoro da sauran da suka haɗa da Uwani Aji, Mohammed Garba, Ibrahim Saulawa, Adamu Jauro, Abubakar Tijjani, da Emmanuel Agim sun amince da korar ƙarar da Atiku da Obi suka ɗaukaka.
To amma bayan wannan hukunci ne da ya kawo ƙarshen taƙaddamar zaɓen, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƴan Ƙasa, Mohammed Idris ya bayyana wa wakilin PUNCH cewar, ƙofar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a buɗe take ga ƴan’adawa.