Rahotanni sun nuna cewa ɗalibai a sassa daban-daban na ƙasar nan sun fara tafiya a ƙafa zuwa makarantunsa sakamakon tsadar kuɗin sufuri da ta biyo bayan ƙarin farashin man fetur.
Yawancin makarantun sun fara sabon zangon karatu a jiya, yayin da wasu za su fara a mako mai zuwa.
Ƙarin farashin man fetur ya shafi kasafin kuɗin iyalai sosai, inda iyaye da dama ke ƙoƙarin samun hanyoyin rage kuɗin makarantar da suke kashewa.
Wasu gwamnatocin jihohi sun ɗaga lokacin fara karatu saboda tsadar sufuri da ke ci gaba da ƙaruwa a ƙasa.
Bincike ya nuna cewa wasu makarantu sun ƙara kuɗin sufuri ko dakatar da motocin ɗaukar dalibai, wanda ya sa iyaye suke tunanin mayar da ƴaƴansu zuwa makarantun da ke kusa da su.
Iyaye sun nuna damuwa game da ƙarin kuɗin abinci da kuma ƙarin kuɗin man fetur, wanda ke sanya tafiyar da rayuwar iyali cikin wahala.
Wani uba a Jigawa ya ce ya fi son ya tabbatar da cewa ƴaƴansa suna da abinci kafin zuwa makaranta, maimakon tura su makaranta ba tare da cikakken abinci ba.
A wasu jihohi, iyaye suna kira ga gwamnati ta daidaita lokacin tura ɗalibai makarantu da zirga-zirgar motocin gwamnati don rage musu wahala.
Rahotanni daga jihohi irin su Taraba, Katsina, Kebbi, da Borno sun nuna cewa ɗalibai da dama suna tafiya a ƙafa zuwa makaranta saboda tsadar sufuri.
Kungiyar masu makarantu masu zaman kansu ta ce suna fuskantar ƙarin kuɗin kayan aiki, amma suna ƙoƙarin sauƙaƙa wa iyaye ta hanyar rage wasu kuɗaɗen.