TSANANIN TSADAR FETUR: Wahala Na Jiran Iyaye, Ɗalibai Da Malamai Yayin Da Ake Shirin Komawa Makarantu

Yayin da makarantu ke shirin fara zangon karatu na 2024/2025 a faɗin Najeriya, ƙarin farashin man fetur da aka samu a makon da ya gabata ya jefa iyaye, dalibai, malamai, da masu makarantu cikin damuwa da tashin hankali.

Wasu masu makarantu masu zaman kansu sun shiga ruɗani kan yanda za su cigaba da gudanar da makarantunsu saboda tsadar kayan aiki, inda ƙarin farashin ya zo bayan sun sanar da iyaye kuɗaɗen makaranta, kuma iyaye na iya bijirewa ƙarin kuɗaɗen kafin ranar buɗe makarantu.

Kamfanin NNPC ya ƙara farashin man fetur daga N580 zuwa N855 a kan kowacce lita, wanda ya jawo ɓacin rai a sassa da dama, inda yanzu ake sayar da man tsakanin N900 da N1,200 a yankunan ƙasar.

Saboda tsadar rayuwa da rashin iya biyan albashin da ya dace ga malaman makarantu masu zaman kansu, wasu malaman sun fara neman wasu aiyukan a gefe, musamman na koyar da darussan Turanci, Lissafi, da Kimiyya tare da ajjiye aiyukansu.

Wannan lamari ya sa wasu makarantu sun rasa malamai masu ƙwarewa a wasu darussa, yayin da har yanzu ake fama da gagarumin giɓin malaman a makarantun gwamnati.

Wani malamin lissafi mai suna Gabriel ya bayyana cewa ya koma koyarwa a makarantu daban-daban don samun ƙarin kuɗin shiga da kuma ƴanci daga takurawar aiki ɗaya.

Iyaye kuma sun shiga neman makarantu masu sauƙin kuɗi a kusa da gidajensu, saboda tsadar sufuri zuwa makarantu masu nisa, wanda ya sa wasu iyayen suka daina tura ƴaƴansu zuwa makarantu masu nisa.

Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT) ta buƙaci gwamnati da ta samar da alawuns na wahala ga malamai, domin tallafa musu wajen shawo kan tsadar rayuwa da tsadar sufurin da ake fama da su a halin yanzu.

Makaranta
Comments (0)
Add Comment