Daga Bala Ibrahim
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa tare da haɗin gwiwar Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) sun ƙaddamar da wani yunƙuri na magance yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.
Jihar Jigawa tana cikin jihohi goma na gaba-gaba a Najeriya da ke da mafi yawan yara da ba sa zuwa makaranta, inda ake ƙiyasin yara kusan 700,000 ke yawon bara, kamar yadda bayanan UNESCO suka nuna.
Wannan shiri ya nuna jajircewar ƴan majalisar dokoki 30 na jihar da gwamnatin jihar wajen fuskantar wannan matsala.
Manufar wannan yunƙuri ita ce rage yawan yara da ba sa zuwa makaranta a duk ƙananan hukumomin jihar 27 da kaso 90% nan da shekarar 2030, bisa manufar cimma burin cigaba na duniya (SDGs).
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da wannan shiri a Ƙaramar Hukumar Miga, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatum, ya bayyana aniyarsu ta ƙoƙarin dawo da yara cikin tsarin karatu.
“A ƙarƙashin shugabancina, mun ƙaddamar da wannan yunƙuri na dawo da yaran da ba sa zuwa makaranta komawa makaranta a duk mazaɓu 30 na jihar nan,” in ji shi.
“Abin da kuke gani a yau an gudanar da shi a sassa daban-daban na jihar nan domin tabbatar da cewa babu yaro ko yarinya da za a bari a waje ba tare da samun damar zuwa makaranta ba.”
Kakakin ya kuma bayyana cewa an dawo da yara 300 makaranta a unguwar Sabuwar Dallan, wanda ya ce wani babban cigaba ne.
“Dawo da yara 300 makaranta a Sabuwar Dallan wata babbar nasara ce a ƙoƙarinmu na ganin duk yara 8,000 masu shekarun zuwa makaranta a Miga sun koma aji. Muna nan daram a kan wannan ƙuduri tare da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da sauran abokan aiki,” in ji shi.
An raba kayan karatu masu mahimmanci ga yaran da suka haɗa da kayan makaranta, jakunkuna, da littattafai a yayin ƙaddamarwar.
Aliyu ya sake jaddada jajircewar majalisar kan cigaba da wannan yunƙuri a faɗin jihar gaba ɗaya.
“Majalisa za ta cigaba da wannan ƙoƙari har sai dukkan yaran Jigawa sun sami damar karatun da ya dace da su,” ya ƙara tabbatarwa.
Wannan yunƙuri ya nuna haɗin gwiwa tsakanin UNICEF, gwamnatin jihar, da ƴan majalisar dokoki domin magance ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen cigaba da jihar ke fuskanta.