Waɗanda Tinubu Zai Naɗa Ministoci Su 15 Ne Kaɗai Daga 28 Suka Gabatar Da Takardunsu

Aƙalla waɗanda za a naɗa ministoci 15 ne suka gabatar da takardunsu ga ofishin Babban Mai Temakawa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Majalissar Dattawa, Abdullahi Gumel zuwa jiya Lahadi.

Waɗansu daga cikin waɗanda sunayensu suka fito a waɗanda Tinubu yake son naɗawa ministocin da aka ga takardunsu sun haɗa da, Shugabar Mata ta APC, Betty Edu;  Uju Ohaneye; Tunde Ojo; Abubakar Danladi, Uche Nnaji; da tsohon Manajan Bankin Nexim  Bank, Stella Okotette.

Wata majiya daga Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa, kusan mutane 15 daga cikin waɗanda za a naɗa ne suka gabatar da takardunsu zuwa jiyan.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Abdullahi Gumel ya sanar da cewa, ana son kowanne wanda sunansa ya fito cikin jerin sunayen waɗanda za naɗa da ya gabatar da takardunsa ga ofishinsa a tsakanin ranakun 28 da 30 na watannan na Yuli.

A yau Litinin ne dai Majalissar Dattawa zata fara tantance ministocin a wani tsari da ta nuna na buƙatar ƙeƙe da ƙeƙe domin sanin tanadin da ministocin suka yi wa Najeriya.

Ministoci
Comments (0)
Add Comment