Wadda Ta Fi Kowa Cin JAMB Ta Samu A Guda 8 Da B Guda 1 A WAEC

Kamsiyochukwu Nkechinyere Umeh, wadda ta samu yabo a duk faɗin Najeriya saboda samun maki 360 a jarabawar JAMB ta shekarar 2023, ta ƙara samun wani abun yabon, inda a jarabawar WAEC da ta fito kwanannan ta samu matsayin A guda 8 da matsayin B guda ɗaya.

A wata wayar salula da jaridar VANGUARD tai da mahaifin Kamsiyochukwu, Mr. Umeh, ya bayyana cewa ƴar tasa ta samu matsayin A1 a darussan Economics, Civic Education, English Language, Further Mathematics, Mathematics, Chemistry, Computer Science da Dyeing and Bleaching.

Umeh ya ƙara da cewar, a darasin Physics ƴar tasa kuma ta samu matsayin B2.

Idan za a iya tunawa dai, Kamsiyochukwu ƴar shekara 16 ta cike neman gurbin karatu a Jami’ar Lagos domin ta karanta Ilimin Kimiyyar Sarrafa Sinadarai wato Chemical Engineering.

JAMBKamsiyochukwuWAEC
Comments (0)
Add Comment