Kusan kwanaki 18 da karewar wa’adinsa na biyu, Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku ya amince da fitar da Naira Biliyan 2 domin siyawa kansa da mataimakinsa da matansu motocin alfarma.
Wata majiya, wadda ta nemi a boye sunanta saboda tsaro, ta shaidawa jaridar PREMIUM TIMES cewa an samu amincewar ne a zaman Majalissar Zartarwar Jihar da ya gabata, wanda Gwamna Darius Ishaku ya jagoranta da kansa.
Majiyar ta bayyana cewa, Gwamnan ne da kansa ya mika bukatar ga Majalissar wadda ta amince kai tsaye ba tare da wani musu ba.
A wajen zaman, an bayyana cewa, tun shekarar 2015 da Darius Ishaku ya zama Gwamnan Jihar Taraba, ya yi ta mafani da motocin da ya gada ne daga tsohuwar gwamnatin da ya gada, abin da ya sa Majalissar ke nan ya cancanci ya samu sabbin motoci a lokacin da yake shirin sauka.
Majiyar ta bayyana cewa, Darius Ishaku da matarsa zasu samu motocin alfarmar da kudinsu ya kai naira biliyan 1.3, yayin da Mataimakinsa da matar Mataimakin zasu samu motocin alfarmar da kudinsu ya kai naira miliyan 750.
Lissafin ya nuna cewa, Darius Ishaku zai samu motoci biyu kirar Toyota Land Cruiser SUV, motocin rakiya guda biyu kirar Toyota Hilux da kuma motar hada-hadar yau da kullum guda daya.
Matar Gwamnan kuma zata samu mota daya kirar Toyota Land Cruiser SUV da kuma motar rakiya guda daya.
Haka kuma shi Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Haruna Manu zai samu motoci biyu na Toyota Land Cruiser SUV masu daraja kasa da na gwamnan da kuma motar rakiya guda daya, yayinda matarsa zata samu Land Cruiser SUV guda daya da kuma motar gudanar da harkokin gida.
Lokacin da aka tuntubi Kwamishinan Yada Labarai ta jihar, Lois Emmanuel, bata musa maganar ba bata kuma tabbatar ba.
Ta dai kawai ce ne, ba ta gari, ta bar jihar sannan kuma bata san labarin ba amma zata bincika, sannan kuma ta katse kiran.
To sai dai kuma, ‘yan awanni kadan bayan hakan, an gano ta tana kaddamar da wani aikin gidaje wadanda gwamnan ya gina a Jalingo, babban birnin jihar.
Darius Ishaku dai ya tsaya takarar Dan Majalissar Dattawa mai wakiltar Taraba ta Kudu, amma ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar APC, David Jim-Kuta.
Yayinda mataimakinsa, Haruna Manu ya nemi takarar Dan Majalissar Dattawa mai wakiltar Taraba ta Tsakiya kuma yai nasara.