Wani Gwamna Ya Musanta Jita-Jitar Komawarsa Jam’iyyar APC, Ya Ce “Ina Nan A PDP Har Abada”

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa yana shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC), yana mai cewa “Ina nan a PDP har abada.”

A wata ganawa da shugabannin PDP na jihar Osun a Osogbo, Adeleke ya ce, “Mutanena, dattawan jam’iyya da shugabanni, ina bayyanawa a gabanku cewa ba zan koma APC ko wata jam’iyya ba, ina nan a PDP.”

A cewar kakakinsa Olawale Rasheed, Adeleke ya bayyana jita-jitar a matsayin “labarin ƙarya” da wasu ke yaɗawa saboda ana jin tsoron irin sauyi da nasarorin da ya samar a mulkinsa.

Taron ya samu halartar dattawan jam’iyyar PDP, kamar tsohon Gwamna Olagunsoye Oyinlola da Shugaban Majalisar Dokokin Osun, Adewale Egbedun, da sauran fitattun ’yan jam’iyyar da suka jaddada goyon bayansu.

Duk da jita-jitar cewa yana shirin neman wa’adin mulki na biyu a zaben shekarar 2026, Adeleke bai bayyana hakan ba a hukumance, amma PDP ta riga ta bayyana goyon bayanta gare shi a matsayin ɗan takarar da zai wa jam’iyyar takara a zaɓen.

PDP ta fuskanci koma baya a baya-bayan nan, inda gwamnoni da ƴan majalisar tarayya suka sauya sheƙa zuwa APC, ciki har da Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, wanda yanzu shine jagoran APC a jihar.

Sai dai PDP ta bayyana cewa hakan na faruwa ne saboda barazana da amfani da dukiyar gwamnati daga APC, yayin da APC ke cewa hakan na nuni da nasarorin gwamnatin Bola Tinubu da muradansa na “Renewed Hope.”

Comments (0)
Add Comment