Wani Sanata Ya Gwangwaje Manoman Mazaɓarsa Da Dubunnan Buhunhunan Takin Zamani A Jigawa

Sanata Babangida Husseini mai wakiltar yankin Jigawa ta Arewa maso Yamma ya raba tireloli 12 na taki kyauta ga manoma a mazaɓarsa domin tallafa wa harkar noma da tabbatar da wadataccen abinci a yankin.

An gudanar da taron ƙaddamar da rabon takin a ƙaramar hukumar Sule-Tankarkar, inda Sanatan ya ce shirin ya gudana ne ƙarƙashin kulawar Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma.

“Kowace ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi 12 a yankin zai samu tirela ɗaya ta taki da za a bai wa manoma da ƙungiyoyin manoman APC da na haɗin gwiwa kyauta,” in ji shi.

WANI LABARIN: Sauya Sunan Jami’ar Maiduguri Zuwa Muhammadu Buhari University Na Shan Suka

Ya kuma ce za ai rabon a dukkan mazaɓu domin tabbatar da cewa ƙananan manoma sun amfana, yana mai jaddada cewa shirin na daga cikin manufofin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da tsaro ta fannin abinci.

Wani manomi daga Gumel, Muhammadu Sani, ya ce: “Muna matuƙar godiya da wannan taimako da ya zo a lokacin da farashin taki ke tashi, kuma wannan zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gonarmu.”

Comments (0)
Add Comment