Wani Tsoho Ɗan Shekara 84 Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Ƙi Kwanciya Da Shi

Wani tsoho ɗan shekara 84 mai ƴaƴa 7 mai suna Gabriel Uhuwa ɗan Jihar Edo ya faɗa komar ƴansanda saboda zarginsa da ake da kashe matarsa saboda ta ƙi yarda ta kwanta da shi.

Ƴansandan ne suka tabbatar da kama tsohon a jiya Laraba, lokacin da suke samamen da suka kamo waɗanda ake zargin ɓata gari ne har su 198.

Waɗanda aka kakkama ɗin dai ana zarginsu da laifuka daban-daban ne da suka haɗa da fashi da makami, garkuwa da mutane, mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, kisan kai, aikata tsafi da sauransu.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ƴansandan, Chidi Nwabuzor ya ce, tsoho Uhuwa da aka kama, an kama shi ne saboda zargin kashe matarsa ƴar shekara 75 saboda ta ƙi yarda ta yi mu’amalar aure da shi.

Jami’in ya ce, sun gano cewar, Uhuwa ya sha fama da matsalar bijirewar matar tasa duk lokacin da ya buƙaci tarawa da ita na tsawon lokaci.

KARANTA WANNAN: Ƴansanda Sun Kama Ɓarayin Wayar Lantarki, Shanu, Awaki Da Ƴan-Fashi A Jigawa

Ya ƙara da cewar, Uhuwa bai yi nadamar abun da ya aikata a kan matar tasa ba, sai ma nuni da yai na cewar hakan da yai shine mafi dacewa ga irin matsalar da ya fuskanta a wajen matar tasa.

Da yake magana da manema labarai, Uhuwa ya ce, matar tasa ba ta ji, duk lokacin da ya buƙaci ta zo su kwanta ba ta zuwa, inda ya ƙara da cewar, suna da ƴaƴa bakwai da matar, biyar maza, biyu mata.

Ya ƙara da cewar, lokacin da matsalar ta dame shi, ya sanar da ɗaya daga cikin ƴaƴansa mata da ta yi wa babar tasu magana don ta gyara, amma hakan bai sa ta gyara ba.

Ya kuma ce, ya kai ƙorafinsa ga danginsa da dangin matar, amma hakan ma bai sa ta gyara ba, sai ta ci gaba da bijire masa, sannan kuma ya samu labarin cewa, malaman coci na kwanciya da ita.

Ya kuma ce, biyo bayan ƙorafinsa da ƴaƴansa suka ji, sun dena turo masa ƴan kuɗaɗen da suka saba turo masa, sannan kuma sun dena ɗaukar wayarsa idan ya kira su, abin da yai zargin cewa, na faruwane saboda zugar da uwar tasu tai musu a kansa.

Ya ce, da abun yai ƙamari ne, yai fushi ya ɗauki adda ya farmaki matar tasa, abun da yai sanadiyyar rayuwarta, abun da ya bayyana a matsayin matsalar fushin da ta sa shi a ciki ne ya janyo hakan, amma bayan ta mutu ya yi nadamar aikata aika-aikar.

AureTsaro
Comments (0)
Add Comment