Wasu Jigajigan PDP Na Zargin Atiku Da Dagula Lamuran Jam’iyyar

Wani mamba na kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP da tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Diran Odeyemi, sun ɗora alhakin rikicin jam’iyyar kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, suna zarginsa da amfani da ƙudirinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 don kawo rabuwar kai a jam’iyyar.

A cewar mamban NWC ɗin, Atiku bai taɓa taka rawar gani wajen ciyar da jam’iyyar gaba ba tun bayan zaɓen 2019 da 2023, sai dai kullum yana ƙara dagula al’amura.

Ya ce “Atiku ne a baya ya ja gwamnonin PDP biyar suka bar jam’iyyar, amma ba ta mutu ba, sannan yanzu yana ci gaba da rura wutar rikici saboda burinsa na 2027.”

WANI LABARIN: Gwamnonin PDP Sun Haɗa Kai Da Wike Don Samar Da Makomar Jam’iyyar Kafin 2027

Odeyemi ya ƙara da cewa Atiku ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen wannan rikici, sai dai hakan na buƙatar ya yi watsi da burinsa na sake takarar shugaban ƙasa, yana mai cewa “duk da cewa yana da ƴancin takara, akwai buƙatar ya sa muradun jam’iyya gaba da muradinsa.”

Sai dai a martaninsa, Atiku ta bakin mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Paul Ibe, ya bayyana zargin a matsayin “marar tushe,” yana mai cewa “akwai mutane da suka haddasa wannan rikici saboda son ransu, yanzu kuma suna ƙoƙarin ɗorawa Atiku laifi don su nemi wata hanya ta kare kansu.”

Ya ce Atiku bai hana kowa takara ba, kuma yana ci gaba da tattaunawa da jiga-jigan jam’iyyar domin farfaɗo da ita.

“Kamar yanda yaron da ya gaza ke ɗora wa mahaifinsa laifi, haka wasu ke ƙoƙarin fakewa da Atiku don ɓoye kura-kuransu,” in ji shi.

Comments (0)
Add Comment