Wata Ƙungiyar Musulmai Ta Dasa Bishiyoyi 2000 A Sabon Ginin FMC, Birnin Kudu

Reshen Ƙungiyar Musulmai ta Jama’atu Nasril Islam, JNI, na Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ya fara dashen bishiyoyi dubu biyu a sabon ginin  asibitin Gwamnatin Tarayya na Federal Medical Centre Birnin Kudu.

Shugaban Sashin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na asibitin, Malam Auwalu Birnin Kudu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikowa TASKAR YANCI.

Sanarwar ta bayyana cewa, Shugaban JNI na Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Malam Magaji Yahuza ya cewa, an samar da wannan shiri ne domin bunƙasa samar da yanayi mai kyau da kare muhalli da barazanar zaizayar ƙasa da kuma samar da muhalli mai daɗi ga masu mu’amala da asibitin.

“Muna yin shirya aiwatar da wannan shiri ne na dashen bishiyoyi domin mu ƙarfafi hukumar asibitin a yunƙurinta na aiwatar aiyukan cigaba a asibitin,” in ji shi.

Ya ce, bishiyoyin da za a dasa sun haɗa da dashe 500 na kowanne daga bishiyoyin Madaci, Zogale, Tsamiya da kuma bishiyar lollipop, tare da yin alƙawarin bayar da kulawa ga shirin har a samu nasarar da ake buƙata.

Shugaban na JNI ya kuma yabawa Shugaban Asibitin kan jajircewarsa wajen ganin cigaban asibitin da kuma halin martaba al’umma.

Ya ƙara da cewa, sama da shekaru ashirin da samar da asibitin, amma iya Dr. Atterwahmie ne kaɗai ya samar da sabon ginin asibitin domin inganta shi.

Shima a jawabinsa, Shugaban Asibitin, Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie ya yabawa ƙungiyar ta JNI da ta zaɓi sabon ginin asibitin domin aiwatar da shirin.

Ya ce, dashen bishiyoyi wata sadakatul-jariya ce wadda ladanta zai samu a nan duniya da kuma lahira.

Ya ce, “Dashen bishiyoyi wani aiki ne mai matuƙar amfani, wadda Annabi Muhammadu S.A.W ya kira al’umma da su rungumi al’adar domin samun ribarsa.”

Ya kuma gargaɗi masu kiwon dabbobi da su guji yin kiwo a yankin da aka dasa bishiyoyin, inda ya ce, zasu ɗau mataki kan duk wanda yai kutse a ginin asibitin.

Atterwahmie ya kuma yi amfani da wannan dama wajen godewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate kan irin gudunmawa da goyonbayan da suke bai wa asibitin.

Shima Malam Aminu Ado Taura wanda shine shugaban Sashin Kula da Muhalli na asibitin, ya tabbatar da cewar za a bayar da kulawa ta musamman ga bishiyoyin da za a dasa.

Ya ce, “Zamu kawo isassun masu kula da bishiyoyi waɗanda zasu na kulawa da bishiyoyin a kullum, saboda kasancewarsu muhimmiyar kadara ga asibitin.

Dr. AtterwahmieFMC Birnin Kudu
Comments (0)
Add Comment