Wike Ya Ce Babu Wanda Ya Isa Ya Kore Shi Daga PDP, Yayin Da Kiraye-Kirayen Korarsa Ke Tayar Da Kura

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi watsi da kiraye-kirayen da wasu ke yi na a kore shi daga jam’iyyar PDP, yana mai cewa ba wanda ya isa ya fitar da shi daga jam’iyyar da ya dade yana yi wa aiki da sadaukarwa.

A wata tattaunawa da manema labarai a Abuja yau Litinin, Wike ya bayyana cewa, “Ni har yanzu ina cikin PDP. Na yi wa jam’iyyar aiki tuƙuru.”

Ya ƙara da cewa, “Ban ga wanda zai iya cewa, ‘Wike ba ka cikin jam’iyya’ ba. Waye wannan? Mene ne gudummawar da ya bayar fiye da ni?”

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rashin jituwa cikin jam’iyyar game da rawar da Wike ke takawa a gwamnatin yanzu da kuma matsayin da ake ganin yana ƙoƙarin samu a siyasa.

WANI LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Bukukuwan Babbar Sallah

Duk da haka, tsohon gwamnan Jihar Ribas ya jaddada cewa yana nan daram a jam’iyyar, kuma ba za a iya korar sa da sauki ba.

Ya ce shi ne ya taimaka wajen samar da ƙarfi da shaharar jam’iyyar PDP tun daga matakin jiha har zuwa na ƙasa.

A martaninsa ga Chief Bode George, mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, game da rufe hedikwatar jam’iyyar, Wike ya ce, “Idan tsoho bai da aikin yi, ya zauna gida yana karanta jarida.”

Dangane da dalilin da yasa ba zai iya biyan kuɗin harajin filin hedikwatar jam’iyyar ba, Wike ya bayyana cewa, “Ba a sanya sunanmu a cikin takardun mallakar gidan ba, don haka ba mu da hurumin biyan kudin.”

A ƙarshe, Wike ya bayyana cewa shi ne ya bai wa jam’iyyar martaba, ba jam’iyyar ce ta ba shi ba.

Comments (0)
Add Comment