Shuagaban Hukumar EFCC, Oala Olukayode ya bayyana cewar, tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya fitar da kuɗi kimanin dala dubu 720,000 daga asusun gwamnatin jihar domin biya wa ɗansa kuɗin makaranta na shekaru masu zuwa.
A lokacin ganawa da manema labarai a Abuja, Olukoyede ya yi zargin cewa, Yahaya Bello ya tura kuɗaɗen ne kai tsaye zuwa asusun wani ɗan canji domin ya biya masa kuɗin makarantar ɗan nasa.
Shugaban EFCCn ya nuna rashin dacewar hakan, inda ya ce, bai kamata gwamna kawai don zai sauƙa daga muƙami ba ya tura kuɗi daga asusun gwamnati zuwa wajen ɗan kasuwa don a biya masa kuɗin makarantar ɗansa.
Olukayode ya ce, shima samun takardun tuhumar Yahaya Bello yai a hukumar EFCC, ba shi ne ya fara lamarin ba.