YAJIN AIKI: Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Dakatar Da Shiga  Yajin Aiki Sai Nan Da Kwanaki 30

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta sanar da dakatar da shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani da ta shirya shiga saboda tsanani.

A baya dai ƙungiyoyin ƙwadago da rassansu na jihohi sun umarci ƴaƴansu a duk faɗin Najeriya da su dakatar da duk wani aiki da suke saboda gazawar gwamnati na biya musu buƙatu bakwai da suka gabatar mata.

A shekaran jiya da jiya Litinin, Gwamnatin Tarayya ta gayyaci ƙungiyoyin ƙwadagon zaman tattaunawa domin magance shiga yajin aikin, zaman da ministoci da wasu gwamnoni suka sami halarta ƙarƙashin jagoranci Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gabajabiamila.

A jawabin bayan zaman jiya Talata, ƴan ƙwadagon sun sanar da dakatar da yajin aikin har sai nan da kwanaki 30.

Sanarwar bayan taron ta kuma buƙaci Ministan Ƙwadago da ya duba lamarin da ya shafi albashin watanni takwas na malaman jami’o’i.

Sanarwar ta samu sahhalewar sa hannun Shugaban NLC, Joe Ajaero da kuma Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja; sannan a kwai sa hannun Shugaban TUC, Festus Osifo da kuma Sakataren TUC, Nuhu Toro.

Wakilan Gwamnatin Tarayya a da suka sanya hannu a takardar sun haɗa da Ministan Ƙwadago, Simon Lalong; Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha da kuma Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris.

NLCTUC
Comments (0)
Add Comment