YAJIN AIKI: Yayin Da NLC Ke Shirin Tsunduma Yajin Aiki, Gwamnatin Tarayya Ta Gayyace Ta Zaman Tattaunawa Gobe Litinin

Gwamnatin Tarayya ta kuma gayyatar shugabancin Ƙungiyar Ƴan Ƙawadago, NLC, zuwa wajen zaman tattaunawa domin magance matsalolin da za su sa ƙungiyar shiga yajin aiki.

An tsara cewar za a gudanar da zaman ne tsakanin ɓangarorin biyu a ranar Litinin 18 ga watan Satumba, 2023.

Sanarwar zaman dai ta fito ne a sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ƙwadago, Olajide Oshundun ya raba a yau Lahadi.

Olajide ya ce, Ministan Ƙwadago da Samar da Aiyukan Yi, Simon Bako Lalong ya ƙara gayyatar Ƙungiyar Ƙwadago domin sake zama a kan yajin aikin da ta ke shirin shiga.

KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Naɗa Jamila Da Ayodele A Matsayin Ministocin Matasa

Ministan ya bayyana cewar zaman yana da matuƙar muhimmanci wajen ganin an magance matsalolin da za su iya kai wa ƴan ƙungiyar ga shiga yajin aiki.

NLC dai na yunƙurin shiga yajin aikin sai baba ta gani ne biyo bayan abun da ta kira da gazawar gwamnati na magance raɗaɗin da al’umma ke ciki a sanadiyyar cire tallafin man fetur.

Tun a farkon watannan ne dai NLC ta sanar da cewar za ta shiga yajin aikin gamagari na sai baba ta gani a cikin makonni uku matuƙar gwamnati ta gaza fito da ƙwararan hanyoyin magance yanayin da ake ciki, abun da ya jawo ta yi yajin aikin gargadi a ranakun 5 da 6 ga wannan watan.

Gwamnatin TarayyaNLCYajin Aiki
Comments (0)
Add Comment