‘Yan Fanshon Da Ke Karbar Naira 333 Duk Wata A Jihar Anambra, Suna Bin Bashin Fansho Na Watanni 11 – NLC

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC reshen Jihar Anambra, Kwamared Humphrey Emeka Nwafor, ya koka kan yadda ‘yan fansho da dama a jihar ke karbar kudin fansho a halin yanzu da bai haura naira 333.45 ba.

Nwafor, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin din nan, a yayin Bikin Ranar Ma’aikata ta Shekarar 2023 da aka gudanar a dandalin Dr. Alex Ekwueme, da ke Awka, babban birnin Jihar Anambra, ya kara da cewa wasu ‘yan fansho na firamare na bin gwamnatin jihar bashin fansho na watanni 11.

Shugaban NLC na Anambra ya ce adadin kudin basussukan fansho na watanni 11 ya kai naira 490,184,626.58.

Ya kuma bayyana cewa, tun a shekarar 2014 ne aka amince za a biya basussukan ta hannun kwamitin hada-hadar kudi na kasa (JAAC) amma har yau ba a yi hakan ba.

Kungiyar NLC a jihar ta kuma yi kira da a soke shirin bayar da gudunmawar fansho a jihar, inda ta ce tun a shekarar 2014, kudaden da aka cire daga albashin ma’aikata ba a kai su wuraren da suka dace ba.

Nwafor ya ce, Kungiyar NLC ta bukaci a ayyana naira dubu talatin (N30,000) a matsayin mafi karancin fansho a jihar lura da halin da ake ciki a yanzu wanda da yawa daga cikin ‘yan fansho ke karbar naira dari uku da talatin da uku, da kobo arba’in biyar (N333.45) a matsayin fanshonsu na wata.

Ya ce, saboda haka, NLC ta bukaci a biya ‘yan fansho malaman firamare bashin watanni goma sha daya (11) daga 2002 zuwa 2003 da suke bi wanda jimillar yawansa ya kai naira miliyan 490,184,626.58.

'Yan FanshoAnambra
Comments (0)
Add Comment