A lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da neman dalilan da ya sa Maryam Shetty ta samu muƙamin minista a matsayinta na matashiya wadda ba tai ƙaurin suna a siyasa ba daga Jihar Kano, labarin canja sunanta ƴan awanni kaɗan kafin shigarta wajen sanatoci domin tantancewa, ya bar bakin mutane a buɗe suna ta nazari kan irin cukumurɗar da ta faru a lamarin, kamar dai yan jaridar DAILY TRUST ta rawaito.
Sunan Shetty dai ya bazu a faɗin ƙasa lokacin da aka ji ta cikin ƙarin ministoci 19 da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya turawa Majalissar Dattawa bayan kammala tantance rukunin farko da ya tura.
To sai dai kuma Shugaban Ƙasar ya bai wa ƴan Najeriya mamaki a ranar Juma’a, lokacin da ya tura wani saƙon ga Majalissar Dattawa yana sanar da su ƙarin sunayen wasu mutum biyu tare da janye sunan Maryam Shetty.
Ita dai Maryam Shetty, ƴar Jihar Kano, an canja sunanta ne da na Dr. Mariya Mahmoud Bunkure, tsohuwar Kwamishiniyar Ilimin Manyan Makarantu ta Jihar Kano, yayinda kuma Shugaban Ƙasar ya tura ƙarin sunan Festus Keyamo, Babban Lauyan Najeriya kuma tsohon Ƙaramin Ministan Ƙwadago sannan kuma Mai Magana da Yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe na Jam’iyyar APC a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, wanda da ma rashinsa a jerin sunayen farko ya tayar da ƙura.
Abubuwan da suka faru a ranar Juma’a har suka jawo janye sunan Maryam Shetty daga cikin ministocin ya matuƙar kaɗa mutane da dama, wannan kuwa na faruwa ne saboda jim kaɗan kafin sanarwar an ga wani gajeren faifan bidiyon da yake nuna ta a Majalissar Tarayya tana dakon tantancewa, faifan kuma ya zaga kafafen sa da zumunta.
Jaridar DAILY TRUST ta tabbatar da ingancin faifan bidiyon daga wani makusancin Maryam Shetty, wanda ya bayyana cewar yana tare da ita a lokacin a Majalissar Tarayya domin tantancewa lokacin da suka ji sabon labarin.
Makusancin nata ya tabbatar da cewar, Shetty ta matuƙar kaɗuwa da jin labarin, nan da nan kuma ta ɗau hanhyar komawa gidanta.
A lokacin da ake haɗa wannan rahoton, ba a samu nasarar riskar Maryam Shetty ba ta kiran waya, saboda layin da aka fi saninta da shi ba ya shiga, yayin da kuma saƙon kar ta kwana da aka tura mata ta hanyar iMessage ya shiga wayarta amma ba ta ce komai a kai ba.
Cukumurɗar Siyasa
Jaridar DAILY TRUST ta tabbatar daga majiyoyi da dama cewar, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda a ranar Alhamis ya zama Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, shine ya bayar da sunan Dr. Mariya Mahmud Bunkure a matsayin wadda za ta maye gurbin Shetty.
Wani makusancin Ganduje ya faɗawa wakilin DAILY TRUST cewa, cukumurɗar siyasar da ta jawo canja sunan Shetty da Dr. Mariya ita ce, ita ba ta cikin ƴan siyasar gidan tsohon gwamnan, inda ya ce, ana zargin wani babban ɗan fadar shugaban ƙasa ne ya kai sunan Shetty.
An gano cewar, an sanar da Ganduje cewar, gurbin da Shetty ta cike, gurbi ne da aka tanada dominsa, saboda haka aka ce ya bayar da wanda zai canje shi, wannan kuwa ya tabbata ne ta hanyar ganin tsohuwar alaƙar da ke tsakanin Abdullahi Tijjani Gwarzo da Bola Ahmed Tinubu tun a tsohuwar jami’iyyarsu ta ACN, wanda shine ɗaya ministan daga Kano.
Saboda haka, tun da Ganduje ya zama shugaban jam’iyya na ƙasa na APC a ranar Alhamis a taron shugabannin jam’iyyar na 12, sannan kuma ya samu labarin cewa, an ƙundundunewa shugaban ƙasa al’amura wajen naɗin Shetty, “sai ya fara ƙoƙarin gyara abin aka ɓata,” in ji makusancinsa.
Shugaban Ƙasar ya yi mamakin cewa, sunan Maryam Shetty ba ta hannun Ganduje ya biyo ba, in ji wata majiya, inda ta ƙara da cewa, “Mutanen da suka bayar da sunanta sun nuna hotonta da tsohon Gwamnan Kanon ga shugaban ƙasa domin su nuna kamar ita ma ƴar gidan siyarsa ce.”
A bayanin yanayin yanda aka miƙa canjin sunan Shetty, wani makusancin Gandujen ya ce, wata hanyar Shugaban Ƙasa ce ta nunawa waɗanda suka miƙa sunan Shetty cewar shi ke da iko da komai, kuma bai ji daɗin abin da ya faru ba.
“Wata kuma hanya ce, ta nuna cewar shugaban jam’iyya na ƙasa yana da girman matsayi a wajen shugaban ƙasa, sannan kuma gargaɗi ne ga duk wanda ya cusa sunanta (Shetty) a jerin sunayen,” in ji majiyar.
Kano dai na ɗaya daga muhimman guraren da jam’iyya mai mulki ta ke so ta riƙa, da kuma wargajewar tattaunawa da Rabiu Musa Kwankwaso, wanda jam’iyyarsa ta NNPP ke mulkin Kano a yanzu, masu nazari sun ce, ta yiwu Tinubu ya yanke shawarar yin amfani da gidan Ganduje wajen kama Kanon.
Haka kuma, wasu majiyoyi na kusa da Shetty sun ce, baya da maganganun da suke cewa, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ne ya bayar da sunanta, wani dalilin da Ganduje yai amfani da shi wajen bayar da canjin sunanta shine, ƙaurin sunan da ta yi wajen adawa da wsu manufofinsa lokacin da yana gwamna, ciki har da batun tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi.
Labari: DAILY TRUST
Fassara: KABIRU ZUBAIRU