Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i a Najeriya, JAMB, ta saki sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2025, inda bayanan hukumar suka nuna cewa sama da kashi 75 cikin 100 na daliban da suka rubuta jarabawar ba su kai maki 200 cikin 400 ba.
JAMB ta ce ana iya duba sakamakon ta hanyar tura sakon UTMERESULT zuwa lambar 55019 ko 66019 daga layin wayar da aka yi rijista da shi lokacin rajista.
Amsar da za a samu daga hukumar za ta bayyana matsayin dalibi, ko sakamako ya fito ko kuwa an dakatar, ko kuwa ba a halarci jarabawar ba, ko kuma an shiga dakin jarabawa ba bisa ka’ida ba.
WANI LABARIN: Ba Za A Ƙara Siyen Kayan Waje A Najeriya Ba Sai In Babu Irinsa A Cikin Ƙasa – Gwamnatin Tarayya
Hakanan, JAMB ta bayyana cewa wanda ke da matsala za a buƙaci ya gabatar da wasu takardu kafin a saki sakamakonsa.
Sauran hanyoyin duba sakamakon sun haɗa da ziyartar shafin eFacility na JAMB a [https://efacility.jamb.gov.ng/login] (https://efacility.jamb.gov.ng/login) tare da amfani da email da kalmar sirrin da aka yi rajista da su.
Bayan shiga shafin, ɗalibi zai iya danna “Check UTME Results” domin ganin makin da ya samu a kowanne fanni na jarabawar.
Hukumar ta ce ita kaɗai ke da ikon bayar da sahihin sakamakon jarabawar, kuma ta gargaɗi ɗalibai da iyayensu da su guji yaudarar masu karya da ke tallata hanyoyi daban-daban da ba su da inganci ko amincewa daga JAMB.