YANZU-YANZU: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Gidajen El-Rufai A Abuja, Sun Tafi Da Wani Magidanci

Mazauna unguwar Kuchiko Resettlement Development Area (KRDA) da ke unguwar Bwari a Abuja sun sanar da yawaitar garkuwa da mutanen da ake yi a unguwar.

Wannan ya biyo bayan lamarin da ya faru da sanyin safiyar yau Asabar, a unguwar da aka fi kira da El-Rufai Estate.

Ƴan bindigar sun tafi da wani magidanci mai suna Chinedu wanda suka kama lokacin yana cikin gidansa a unguwar.

Matar magidancin ta bayyana cewar, masu garguwa da mutanen suna ɗauke da manyan makamai, sannan sun haura katanga inda suka samu damar shiga gidan nasu.

KARANTA WANNAN: JERIN SUNAYE: Sojojin Da Suka Mutu Sanadiyar Harbo Jirginsu Da Ƴan-Ta’adda Suka Yi A Neja

Jaridar DAILY TRUST ta rawaito matar tana cewa, maharan sun yi harbin kan mai uwa da wabi inda suka tsorata kowa kafin daga bisani su tafi da mijin nata.

Shugaban unguwar, Mai Baba Bego, wanda yai magana kan lamarin ya ce, cikin ƴan watanni kaɗan da suka gabata, an yi garkuwa da mutane 5 a unguwar.

Ya ƙara da cewar a yanzu haka suna rayuwa cikin firgici, domin ba su san kan wa abin zai faɗa a gaba ba.

Ba a samu Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Babban Birnin Tarayya ba kan lamarin saboda wayarsa ba ta shiga har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Garkuwa da Mutane
Comments (0)
Add Comment