Ibrahim Garba Ibrahim, mai temakawa Gwamnan Jigawa Umar Namadi a ɓangaren wayar da kan jama’a kan harkokin siyasa, ya sauƙa daga muƙaminsa a wata wasiƙa da ya aike wa gwamna mai ɗauke da kwanan watan 22 ga Agusta, 2025.
A cikin wasikar ya rubuta, “na sauƙa daga muƙamina na Mai Temakawa Gwamna a Ɓangaren Wayar da Kan Jama’a Kan Harkokin Siyasa, daga yau 22 ga Agusta 2025,” yana mai cewa ya yi hakan ne domin komawa harkokin kasuwancin da ke buƙatar lokacinsa.
Ya ƙara da cewa zai ci gaba da kasancewa ɗan jam’iyyar APC kuma zai ci gaba da goyon bayan jam’iyyar ba tare da tsayawa ba.
A ranar 11 ga watan nan kuma Zakari Kafin Hausa, Mai Temakawa Gwamna a Ɓangaren Lafiya, ya ajjiye muƙaminsa bayan yawan fitowarsa yana sukar yadda ake tafiyar da al’amura a gwamnatin jihar.
A ranar 19 ga watan nan gwamna Umar Namadi ya tsige Mai ba shi Shawara kan Harkokin Majalissar Tarayya, Rabi’u Garba Kaugama, matakin da ya jawo tambayoyi kan dangantakar gwamna da masu masa hidima.
Ana ta raɗe-raɗin cewar akwai rarrabuwar kai a cikin APC a jihar tsakanin mabiya tsohon gwamna Badaru Abubakar da ɓangaren gwamna Umar Namadi, lamarin da ka iya sake tada ƙura a siyasar jam’iyyar.
Ibrahim Garba ya bayyana godiyya ga gwamna bisa damar da ya ba shi, “Ina godiya ga zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Jigawa bisa ba ni dama da yai na yi aiki a gwamnatinsa,” in ji wasiƙar.