Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Dr. Jamila Bio Ibrahim da Mr. Ayodele Olawande a matsayin ministocin da za su jagoranci Ma’aikatar Matasa ta Tarayya.
Sanarwar naɗin na su ta fito ne a wani jawabi da Mai Bayar da Shawara na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kafafen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Ajuri Ngelale ya saki a yau Lahadi.
Idan har sanatoci su ka tabbatar da sunayen mutane biyun, Jamila za ta zama Babbar Ministar Matasa, yayin da Ayodele zai zama Ƙaramin Ministan Matasa.
Fadar Shugaban Ƙasar ta bayyana Dr. Jamila Ibrahim a matsayin matashiyar likita da ta yi fice.
A baya ta taɓa zama Shugaban Ƙungiyar Progressive Young Women Forum (PYWF).
Ta kuma riƙe muƙamin Babbar Mai Bayar da Shawara ga Gwamnan Jihar Kwara kan Sustainable Development Goals (SDGs).
KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Karya Dokar CBN Wajen Naɗa Madadin Emefiele, In Ji Wani Lauya
A ɗaya ɓangaren kuma, Ayodele ƙwararren masanin harkokin ciyar da al’umma gaba ne, kuma shugaban matasa a jam’iyyar APC.
Ya riƙe muƙamin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Ƙirƙire daga shekarar 2019 zuwa 2023.
A baya dai Shugaban Ƙasa Tinubu ya rantsar da ministoci 45 a ranar 21 ga watan Agusta, yayin da aka jira sunan wanda zai maye gurbin Nasir El-Rufai daga Jihar Kaduna.
A yanzu dai ministocin Tinubu sun kai 49 kenan idan aka ƙara da waɗannan sabbin guda biyu, adadin da wasu ke ganin ya yi yawa kuma zai laƙume arziƙin ƙasa.