YANZUNNAN: Zanga-Zanga Ta Barke A Abuja Kan Karancin Fetur

Wasu masu zanga-zanga sun mamaye titunan Abuja a yau Litinin suna neman a sauke Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, bisa matsalar karancin fetur da ke addabar kasar.

Zanga-zangar ta biyo bayan amincewar Kamfanin Man Fetur na Najeriya da cewa akwai ɗinbin bashi da ke kansa wanda masu kawo fetur ke bi, wanda kuma ke barazana ga cigaba da samar da man fetur yadda ya kamata a kasa.

A cikin bayanan kamfanin, sun nuna cewa wannan matsin bashin na janyo babbar matsalar kan ayyukansu kuma yana barazana ga zaman lafiyar rarraba man fetur.

Lauyan kare hakkin dan’adam, Femi Falana, ya bayyana damuwa kan cewa karuwar tsadar rayuwa, kara farashin fetur a matatun mai, da karancinsa ya haifar da raguwar motocin da ke bin hanyoyin Najeriya.

Falana, wanda ya bayyana wannan yayin da yake tattaunawa a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, ya kuma bayyana cewa lokaci ya yi da za a bankado ‘babbar zamba’ da ke addabar shigo da fetur Najeriya.

Yayin da suke rera wakokin hadin kai tare da nuna tutoci da suke dauke da rubuce-rubuce kamar “Mun gaji da karancin fetur da labaran da ake yi kan rashin aiki na matatun mai,” “Babu shugabanci mai kyau a wajen Kyari,” da “Muna son gaskiya a harkokin NNPCL,” masu zanga-zangar sun koka da cewa wa’adin Kyari ya kasance cike da rashin nasara da ke haifar da karin tambayoyi fiye da amsoshi ɓangaren man fetur a ƙasa.

Da yake jawabi ga manema labarai a Unity Fountain bayan taron gangamin a Abuja, Shugaban Kungiyar Hadin Kan Kungiyoyin Farar Hula, Aminu Abbas, ya yi mamakin yanda kasa mai arzikin man fetur irin Najeriya za ta ci gaba da fama da matsalar karancin fetur.

Ya ce, “Ga Shugaba Ahmed Bola Tinubu da dukkan wadanda ke kan madafun iko, muna cewa lokaci ya yi da za ku dauki mataki. Ku nuna mana cewa kuna tare da talakawa. Dole ne a sauke Kyari daga kujerarsa, kuma a sake fasalin NNPCL don ta yi aiki don amfanin dukkan ‘yan Najeriya. Ba za mu yi shiru ba.

“Karancin fetur da muke fuskanta a yau an tsara shi ne domin kara mana wahala. A karkashin jagorancin Kyari, al’amura sun kara tabarbarewa, kuma babu alamun gyara. Me ya yi don rage wannan matsala? A bayyane yake cewa yana nufin cigaba da wani tsarin da ke amfanar da wasu ‘yan tsiraru ne kawai yayin da talakawa ke fama da wahala.”

NNPCL
Comments (0)
Add Comment