Hukumar Kula da Yara ta Majalissar Ɗinkin Duniya, wato UNICEF, ta bayyana cewa yara miliyan 3.5 a Najeriya na fama da tsananin matsalar rashin abinci mai gina jiki, inda wasu 400,000 daga cikinsu ke fuskantar barazanar mutuwa cikin wata guda da kwana takwas idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
Babban jami’ar ayyukan UNICEF a Najeriya, Judith Leveille, ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja, inda ta ce “muna da wata ɗaya da kwana takwas kafin mu fuskanci cikas wajen samun kayan magani masu muhimmanci”.
Ta bayyana cewa, kayan da ake buƙata sun haɗa da abinci irin na magani da ake amfani da shi wajen ceto rayuwar yara masu fama da matsananciyar yunwa, tana mai cewa “a cikin yaran nan akwai wanda zai iya zama masanin kimiyya ko mawaƙi sananne a ƙasa.”
Ta bayyana cewa a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, cibiyoyin da ke kula da yara masu fama da yunwa sun cika maƙil, kuma “ba mu kai ƙololuwar lokacin yawan samun matsalar ba, amma har yanzu akwai ƙarancin ma’aikata da kayan aiki.”
Daraktar INGO Forum a Najeriya, Camilla Higgins, ta bayyana cewa “adadin yaran da ke cikin wannan halin ya kai ciki 60 na cikar filin wasa na ƙasa a Abuja gaba ɗaya.”
WANI LABARIN: Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Wata Muhimmiyar Hukuma A Jigawa
Higgins ta ce an samu raguwa a tallafin da ake samu daga manyan ƙasashen duniya kamar Amurka, lamarin da ya haddasa raguwar ƙoƙarin bayar da agaji, musamman a yankunan da rikici ya fi ƙamari.
A cewar shugaban MSF a Najeriya, Bilal Ahmad, “mun fara ganin ƙaruwar yawan yara da aka fi tsammanin za su zo ne a ƙarshen damina, amma yanzu haka suna zuwa tun a farkon daminar.”
A cewarsa, akwai matuƙar ƙarancin gadajen kwanciya a cibiyoyin jinya, inda a wasu wuraren ake sa yara biyu a gado ɗaya, har ma a wasu wuraren ana ƙara adadin yaran a kan gado ɗaya.
A ƙarshe, Ministan Harkokin Jinƙai, Dr Yusuf Sununu, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasa da ƙasa domin tabbatar da gaskiya da nagarta a ayyukan agaji da jinƙai a Najeriya.