Daga Mika’il Tsoho, Dutse
A wani abin yabo don tunawa da Ranar Yara ta Duniya ta 2024, yara a Jihar Jigawa tare da tallafin UNICEF sun karɓi iko a Majalisar Jiha don neman haƙƙoƙinsu da makomarsu.
Zaman majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugabar Majalisar Yara, Jamila Aliyu Abdulkadir, ya tattauna kan muhimman batutuwa irin su dokokin kare yara, inganta ilimin ƴan mata, da rage yawan yaran da basa zuwa makaranta a jihar.
Da take jawabi ga majalisar, Shugabar Majalisar Jamila ta yi kira ga gwamnati, iyaye, da masu ruwa da tsaki su tallafawa yara wajen cimma burinsu, tana mai jaddada matsayinsu a matsayin shugabannin Jigawa da Najeriya na gaba.
“Muna kira ga kowa da ya taimaka mana mu cimma burikanmu kuma mu mayar da Jigawa wata alama ta cigaba,” in ji ta.
UNICEF Nigeria, a cikin wata sanarwa da ta yi yayin bikin, ta jinjina wa yaran kan halartar su sannan ta buƙace su da mayar da hankali kan ilimi da kyawawan halaye.
“Kuna a matsayin shugabannin gobe. Ku dage da karatunku ku kuma guji sharrin da ka iya ɓata muku tarbiya,” inji sanarwar.
Ranar Yara ta Duniya, da ake bikin ta a duk shekara a ranar 20 ga Nuwamba, tana tunawa da karɓar Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan Hakkin Yara a 1989.
Taken shekarar 2024, “Jin Muryar Gobe,” yana haskaka mahimmancin muryar yara wajen gina kyakkyawar makoma.