Yawan Dogaro Da Bashi Ya Zo Ƙarshe A Najeriya – Tinubu

A jiya Talata ne a Abuja, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Tsare-tsaren Kashe Kuɗaɗe da Sake Fasalin Karɓar Haraji, inda ya ce, yawan dogaro da bashi wajen kashe kuɗaɗen gudanar da gwamnati ya zo ƙarshe.

Ya koka kan yawan kuɗaɗen da ake warewa domin biyan basussukan da aka ci yo, inda ya ce, suna matuƙar wahalar da kuɗaɗen shigar da gwamnati ke samu.

Kwamitin Shugaban Ƙasar kan Tsare-tsaren Kashe Kuɗaɗe da Sake Fasalin Karɓar Haraji ya samu shugabancin Taiwo Oyedele.

Da yake baiwa mambobin kwamitin aiyukansu, Shugaban Ƙasa Tinubu ya buƙace su da su ƙara yawan kuɗaɗen da ƙasa take samu da kuma faɗaɗa harkokin kasuwancin gwamnati, musamma ma a lokacin da Gwamnatin Tarayya ke ƙoƙarin ƙara yawan harajin da take samu.

Shugaban Ƙasar ya umarci kwamitin da ya sauƙe nauyin da aka ɗora masa a shekara guda na samar da kyakkyawan tsarin kashe kuɗaɗen gwamnati, sake fasalin karɓar haraji, da kuma samar da ci gaba a fannin samun kuɗaɗe.

Ya kuma umarci dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomi da su bayar da cikakken haɗin kai ga kwamitin domin samun nasarar aiyukansa.

Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa, aikin kwamitin yana da matuƙar muhimmanci ga gwamnatinsa, musamman ma ganin irin sa ran da ƴan ƙasa suka ɗorawa gwamnatin na ta inganta rayuwarsu.

BashiBola Ahmad TinubuTattalin Arziki
Comments (0)
Add Comment