ZAƁEN CIKE GURBI: Ana Zargin Ma’aikatan INEC Da Wani Shugaban PDP Da Siyen Ƙuri’u, Yayin Da Zamfara Da Kaduna Suka Fuskanci Rikici Da Ƙarancin Masu Zabe

Rundunar ƴan sanda ta kamo manyan PDP biyu ciki har da shugaban jam’iyyar a Iperu, Alhaji Abayomi Tella, tare da ma’aikatan INEC biyu da ake zarginsu ta tanadar kuɗi domin sayen ƙuri’a a zaɓen Remo Federal Constituency.

Wani rahoto ya ce waɗanda aka kama ɗin ana zargin sun ba ƴan sanda muhimman bayanai game da rawar da kowannensu ya taka a kan shirin aikata zamba, sai dai PDP ta musanta, tana mai cewa an kama Tella a otel ɗinsa ne a wani yunƙuri na raunana gwiwar adawa, tare da zargin cewa ana son ba APC dama ne a zaɓen.

A dai dai lokacin da ake ta wannan rigima, Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya jefa kuri’a a PU 002, Ward 3 Ita-Osanyin, Iperu, inda ya yabawa yadda INEC ta shirya aikin, yana mai cewa, “A safiyar yau, a zaɓen cike-gurbi na Remo Federal Constituency, na cika haƙƙin da ke kaina na siyasa ta hanyar jefa kuri’a a PU 002, Ward 3, Ita-Osanyin, Iperu, a Ikenne LGA”.

Gwamnan ya ƙara da yabawa yanayin zaman lafiya da tsari da ya bayyana a rumfunan zaɓe, inda ya ce, “Ina yabon zaman lafiya da yadda lamuran suka tafi, da kuma irin shirin da jami’an INEC suka nuna a rumfunan zaɓe”.

A Zamfara kuwa, an ce zaɓen Kaura-Namoda ta Kudu ya gudana cikin lumana a yawancin wurare tare da cikar masu kaɗa kuri’a, sai dai an samu cinikin ƙuri’u da nufin janyo masu kaɗa kuri’a a wasu rumfuna da kuma tashin hankali a Makarantar Firmare ta Kasuwar Daji inda aka soke zaɓe a wasu rumfuna saboda ƴan daba.

A Kaduna, duk da tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka, an ga ƙarancin masu fitowar masu zaɓe a rumfunan Sabon Gari, Zaria, Chikun da Kajuru, yayin da wani jami’in INEC da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Mun iso kan lokaci don fara kaɗa kuri’a, amma ku gani da kanku cewa masu zaɓe ba su zo kamar yadda ake tsammani ba”.

Wasu mazauna sun bayyana dalilan rashin fitowar da cewa “mutane suna cikin yunwa kuma sun fi son zama a gida saboda tsoron hari”, in ji Sarah Musa daga Chikun, yayin da wasu suka ce an samu ƙarancin sanarwa daga kafafen yaɗa labarai game da zaɓen.

Kodayake an umurci taƙaita zirga-zirga a wasu sassan jihar kamar yadda rundunar ƴan sanda ta sanar, mutane da dama sun ci gaba da zirga-zirga kamar babu wani umarni, lamarin da ya sa wasu ke zargin cewa tsaro da shirye-shiryen wayar da kai ba su isa ba.

Tun da yake INEC ta shirya ɗaukar matakai na samun sakamako mai kyau, masana da masu sa ido na sa ran abubuwa za su bi tsarin doka, amma abin da ya faru a Iperu da wasu yankuna ya jawo cece-kuce da kira ga gaggauta bincike domin tabbatar da cewa muradin masu kaɗa ƙuri’a ne ya tabbata.

Comments (0)
Add Comment