Gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da ciwo bashi don cike kasafin kuɗi, duk da cewa an zarce hasashen kuɗaɗen shigar da akai tsammani a wasu bangarori, in ji Ministan Kudi, Wale Edun.
Da yake magana a gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa kan Kuɗi da Tsare-tsare, Edun ya bayyana cewa ciwo bashin ya zama dole domin samar da muhimman ayyuka da abubuwan more rayuwa.
“Duk da cigaban da aka samu a kuɗaɗen shiga, ba su isa ba. Dole ne bashin da za a ciwo ya zama mai amfani da ɗorewa, musamman a fannonin lafiya, ilimi, da walwalar jama’a,” in ji Edun.
Ministan Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi, Sanata Atiku Bagudu, ya kara da cewa kasafin kuɗi na 2024, wanda ya kai Naira tiriliyan 35.5, yana ɗauke da giɓin Naira tiriliyan 9.7, wanda hakan ya sa za a nemi bashin waje.
Sai dai Hukumar EFCC da Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga sun bayyana cewa inganta tara kuɗaɗen shiga na iya hana buƙatar ciwo bashin.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa an ƙwato sama da Naira biliyan 197 a bana, yayin da Shugaban Kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce an samu ƙarin kuɗin shiga har Naira tiriliyan 5.352, wanda ya zarce abin da aka sa ran samu.
Hakazalika, Kamfanin Man Fetur na NNPCL ya samu Naira tiriliyan 13.1, wanda ya zarce hasashen abun da aka tsara zai samu.
Duk da waɗannan nasarori, masu suka, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, sun yi tir da shirin ciwo bashin da cewa bai da amfani kuma yana da tasiri kan yawaitar samun cin hanci.
“Waɗannan basussuka suna ƙara matsin lamba ga al’ummar Najeriya,” in ji shi a wata wallafa da yai a shafin X, inda ya buƙaci a samar da tsarin mai kyau wajen sarrafa kuɗaɗen gwamnati.