Za A Iya Sayar Da Man Dangote Ƙasa Da Naira 600 Matuƙar Gwamnati Ta Bi Shawarar Wata Ƙungiya

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya, IPMAN, ta bayyana cewa mambobinta za su gana da Matatar Dangote a wannan makon don tattaunawa kan fara ɗaukar man fetur kai tsaye daga kamfanin da kuma rage musu farashin man.

Mai magana da yawun IPMAN, Chief Chinedu Ukadike ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, yana mai cewa mambobinsu suna sa ran fara ɗaukar man fetur daga Matatar Dangote nan kusa.

A cewarsa, samar da isasshen man fetur ya zama babban kalubale a ɓangaren man fetur da iskar gas na Najeriya, duk da cewa an fara fitar da man Dangote.

Wannan maganar dai ta biyo bayan yanda gidajen mai na NNPC da sauran masu sayar da man fetur ke sayar da man fetur tsakanin naira 950 da Naira 1,100.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Masu Sarrafa Danyen Man Fetur ta Najeriya, CORAN, ta buƘaci gwamnatin Najeriya ta tsayar da farashin musayar kudi a naira 1,000 kan kowacce dala, domin rage farashin man da Dangote ke fitarwa zuwa ƙasa da naira 600 kan kowacce lita.

CORANIPMANMatatar DangoteTsadar Man Fetur
Comments (0)
Add Comment