Zamu Fara Shirin Ɗiban Dubunnan Ƴansanda A Najeriya – Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin samar da kayan aiki na zamani ga Hukumar Ƴansandan Najeriya domin inganta ayyukanta.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne ya bayyana hakan a yayin bikin yaye ɗalibai 478 a Kwalejin Ƴansanda ta Najeriya da ke Wudil a Jihar Kano.

Tinubu wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya jaddada muhimmancin gujewa cinhanci da riƙon gaskiya wajen gudanar da ayyuka.

Ya ce, “Muna shirin fara ɗaukar matasa da yawa aiki a cikin ƴansanda domin su taimaka wajen tabbatar da tsaron ƙasa.”

Shugaban Ƙasar ya yi kira ga sabbin jami’an da su yi aiki bisa ƙa’idojin aikin ƴansanda na zamani tare da nuna yaƙinin cewa jami’an sun samu isasshen horo da ilimi da zai taimaka wajen kyautata tsarin tsaron ƙasa.

Tinubu ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tallafa wa kwalejin, wadda ya kira a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun cibiyoyin horas da ƴansanda a yankin Afirka Ta Kudu da Hamadar Sahara.

Bola Ahmed Tinubu
Comments (0)
Add Comment