Zargin Aikata Biɗala: Jami’in Hisbah Na Kano Ya Musanta Jita-Jitar Ƙarya A Kan Kwamishinan Jigawa Da Aka Dakatar

Daga Mika’il Tsoho, Dutse

Wani jami’i na rundunar Hisbah ta Jihar Kano mai kula da yankin Yankaba a cikin birnin Kano, Malam Aliyu Usman, ya musanta wata murya da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda ake ikirarin cewa Hon. Auwal Sankara ya amsa cewa yana da haramtacciyar alaƙa da wata matar aure.

Malam Usman ya bayyana wannan sauti a matsayin na ƙarya.

A yayin da yake fayyace batun, Malam Aliyu Usman ya bayyana cewa sun samu ƙorafi ne daga mijin matar.

Bayan da suka gudanar da bincike kuma, sun same ta a cikin mota, yayin da aka hango Hon. Auwal Sankara yana tafiya zuwa ƙofar gidan tare da mai gadin gidan.

“Ina matsayin ƙaramin jami’i; ba ni da ikon yin magana, bayyanawa ko kuma bayar da rahoto ga kowane mutum dangane da ayyukanmu, sai dai babban jami’inmu, Malam Mujahid. Don haka abin mamaki ne daga ina wannan sautin da aka jingina min ya fito,” in ji Malam Usman.

Da yake tsokaci kan batun, lauya mai kare matar, Barista Rabiu Shuaibu Abdullahi, ya ce an kai batun kotu, inda wadda yake karewa take matsayin wadda ke kare kanta ta biyu.

Barista Rabiu ya ƙara da cewa kotu ta umarci Sufeto-Janar na ƴan sanda ya gudanar da bincike kan lamarin, kuma suna farin ciki da hukuncin da kotun ta yanke.

Lauyan ya kuma bayyana cewa akwai matsalolin zamantakewa tsakanin ma’auratan tsawon shekaru, har zuwa wani matakin da mijin, wanda shi ne mai ƙorafin, ya kasance yana amfani da bindiga don tsoratar da matarsa a lokacin da suke rikici.

“Wadda nake karewa tana da gidan abinci a Lamido Crescent wanda aka san shi sosai. Ana yawan yin odar abinci daga wurinta, amma saboda rikicin aurenta, mijinta ya saka mata na’urar leƙen asiri don bibiyar duk wani motsinta ba tare da wani dalili ba sai don ya takura mata,” in ji Barista Abdullahi.

Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin daga sashen binciken manyan laifuka na jihar Kano (CID), yayin da Kwamishinan da aka dakatar, Hon. Auwal Dalladi Sankara, ya sha alwashin ganin an kai ƙarshen binciken don tsarkake sunansa da na iyalinsa.

Kano HisbahSankara
Comments (0)
Add Comment