Zargin Kisa: Wanda Ake Tuhuma Da Kashe Jami’in Civil Defense Ya Mutu Yayin Yunƙurin Tserewa

Daga: Mika’il Tsoho, Dutse

Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta bayyana kama wani mai suna Salisu Muhd mai shekaru 45, da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa jami’insu, Bashir Adamu Jibrin, a kasuwar Shuwarin a ƙaramar hukumar Kiyawa, amma lamarin ya ƙare da mutuwar wanda ake zargin yayin ƙoƙarin tserewa.

A cewar sanarwar da ASC Badaruddeen Tijjani, ya fitar a Dutse ranar Asabar, jami’in da ya rasu ya mutu ne yayin da yake gudanar da aikinsa na kama wanda ake zargi, bayan samun “bayanin sirri mai inganci” kan cewa Salisu ya bugi marigayin da dutse a ka har ya samu rauni mai tsanani.

An ce an samu nasarar kama Salisu a gidansa da ke Shuwarin a ranar 7 ga Agusta 2025, amma yayin da ake ɗaukarsa cikin motar hukumar zuwa cibiyar Civil Defense a Dutse, sai ya “faɗo daga cikin motar da niyyar tserewa daga hannun hukuma.”

Wannan, in ji sanarwar, ya sa ya faɗi ƙasa ya ji munanan raunuka kuma bai iya gudu ba, lamarin da ya sa jami’an suka garzaya da shi zuwa Asibitin Gwamnati na Dutse domin ba shi kulawar gaggawa.

Likita a asibitin ya tabbatar da mutuwarsa, amma ƴan uwansa sun dage sai an samu rahoton likita daga Sambo Hospital Limited, inda binciken ya nuna cewa “ya mutu ne yayin ƙoƙarin tserewa yayin da motar ke gudu sosai.”

Hukumar ta jaddada cewa mutuwar ta faru ne sakamakon yunƙurin tserewa daga cikakkiyar tsarewar doka, abin da ya tayar da hankalin jama’a a yankin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kira da a ƙara tsaurara matakan tsaro a kasuwannin jihar domin kare rayukan jami’an tsaro da ƴan kasuwa.

Comments (0)
Add Comment