Zulum Ya Jagoranci Maidowa Da ’Yan Gudun Hijira Daga Chadi

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya jagoranci dawowar ’yan gudun hijira da suka tsere daga rikicin Boko Haram zuwa Baga Sola a Jamhuriyar Chadi.

Wadanda suka dawo sun hada da iyalai 1,768 da suka kunshi mutum 7,790 da aka tsugunar na kusan shekaru goma a can. 

Tawagar gwamnatin Najeriya ta hada da Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Dr. Yusuf Tanko Sununu, da Shugaban Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira, ’Yan Ci Rani da Masu Hijira (NCFRMI).

Gwamna Zulum ya tabbatar da cewa kawai wadanda suka nuna sha’awa ne za a dawo da su, inda ya gode wa gwamnatin Chadi bisa karbar ’yan Najeriya da suka gudu daga rikicin da ya auku.

A bangaren sa, Ministan Jin Kai, Dr. Sununu, ya yaba da yadda Gwamna Zulum ke hada kai da gwamnatin tarayya don magance matsalar gudun hijira. 

Wannan matakin ya nuna kudirin Najeriya na tabbatar da tsaro da inganta rayuwar ’yan gudun hijira da suka dade a sansanonin waje.

Comments (0)
Add Comment