Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

An Bindige Jami’in NDLEA Har Lahira Yayin Da Yake Bakin Aiki

Wasu da ake zargin masu fataucin miyagun ƙwayoyi ne sun bindige wani jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), mai suna Jide, a wani samame da aka kai a unguwar Ita’nla da ke garin Ondo.

Rahotanni sun ce jami’an NDLEA sun kai farmaki gidan da ake zargin an ɓoye ƙwayoyi a cikin rufin gidan, inda suka gamu da hari daga wasu da ba a gane su ba.

“Ana kyautata zaton jami’an NDLEA sun samu bayanan sirri cewa ana ajiye ƙwayoyi a gidan, shi ne suka je domin cafke su,” in ji wani da ke kusa da hukumar.

Lokacin da wasu daga cikin jami’an suka shiga cikin gidan domin gano ƙwayoyin, Jide ya tsaya a waje yana gadin hanya, sai ga wasu inda suka fito kwatsam suka buɗe masa wuta.

WANI LABARIN: Har Yanzu Sanata Natasha Dakatacciya Ce – Majalissar Dattawa

An harbe shi a wuyansa, inda aka garzaya da shi asibiti amma likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu tun kafin a iso da shi wajensu.

Kakakin rundunar ƴansanda na jihar, Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a harin.

“Mun gano bindiga ƙirar single barrel a wurin, kuma bincike na ci gaba da gudana tare da haɗin gwiwa da hukumar NDLEA,” in ji shi.

Ya ce an tura ƙarin jami’ai zuwa wurin domin tabbatar da zaman lafiya da kuma bin sawun waɗanda suka tsere.

Har yanzu dai, hukumar NDLEA ba ta fitar da sanarwa kai tsaye ba, amma jama’a na nuna damuwa kan irin haɗarin da jami’an tsaron ke fuskanta a yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi.