Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

An Damƙe Mai Yin Takin Zamanin Bogi, Yana Sawa A Buhun Takin Zamanin Gaske

Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya, SON, a Jihar Bauchi ta ce, jami’anta sun damƙe wani mai sarrafa takin zamanin bogi a garin Chinade da ke Ƙaramar Hukumar Katagum ta jihar.

Hukumar ta kuma ce, ta samu nasarar ƙwace aƙalla buhunhunan takin zamanin bogi 150 a shagon mai laifin da ke garin na Chinade a ranar Asabar ta makon jiya.

Shugaban SON na Shiyyar Arewa maso Gabas, Adamu Abba, wanda ya gana da wanda ake zargin kafin ƴan jaridu a yau Asabar ya ce, an kama mai laifin ne yana yin takin zamani na Golden Fertilizer abuhunhuna kala huɗu da suka haɗa da Mai Rago, Freedom, Boko da kuma Indorama.

Labari Mai Alaƙa: Sama Da Ƴan Afirka Miliyan 300 Ne Ke Kwana Da Yunwa A Kullum

Ya ƙara da cewa, an kama shi ne a dai-dai lokacin da yake zuba takin bogin a buhunhunan Golden Fertilizer da nufin siyarwa manoma a matsayin takin gaske.

Shugaban sintiri na SON a yankin, Murtala Sa’ad ya ce, za a miƙa wanda ake zargin ga kotu domin yi masa hukuncin da ya dace.

Wanda ake zargin mai suna, Alhaji Ibrahim Ahmed Chanade, ya faɗawa ƴan jarida cewa, rashin sanin doka da kwaɗayin son yin kuɗi da wuri ne suka kai shi ga aikata laifin, inda ya roƙi SON da tai masa afuwa.