Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

An Damfara Tinubu A Kotu Kan Ƙin Hana Badaru Da Wasu Tsofin Gwamnoni Karɓar Fansho

Ƙungiyar Tabbatar da Gaskiya da Kare Haƙƙin Al’umma a Zamantakewa da Tattalin Arziki ta SERAP ta shigar da ƙarar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan gazawarsa na dakatar da tsofin gwamnonin da ya naɗa ministoci daga karɓar fansho da sauran kuɗaɗen ritaya daga jihohinsu alhalin su na aiki a matsayin ministoci.

Ministocin da aka bayyana a ƙarar sun haɗa da Badaru Abubakar (tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma Ministan Tsaro mai ci); Nyesom Wike (tsohon gwamnan Jihar Rivers kuma Ministan Birnin Tarayya) David Umahi (tsohon gwamnan Ebonyi kuma Ministan Aiyuka mai ci).

Sauran sun haɗa da Bello Matawalle (tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma Ƙaramin Ministan Tsaro); Adegboyega Isiaka Oyetola (tsohon gwamnan Jihar Osun kuma Ministan Sufuri); Simon Bako Lalong (tsohon gwamnan Jihar Plateau kuma Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi); Atiku Bagudu (tsohon gwamnan Jihar Kebbi kuma Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Bunƙasa Tattalin Arziƙi); da kuma Ibrahim Geidam (tsohon gwamnan Jihar Yobe kuma Ministan Harkokin Ƴansanda).

KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Karya Dokar CBN Wajen Naɗa Madadin Emefiele, In Ji Wani Lauya

A watan Agustan da ya gabata dai, SERAP ta buƙaci Tinubu da ya umarci tsofin gwamnonin da su daina karɓar fansho, motocin ban girma da sauran alawuns daga jihohinsu alhalin su na aiki a matsayin ministoci.

Ta kuma buƙaci shugaban ƙasar da ya umarci tsofin gwamnonin da su mayar da kuɗaɗen fanshon da sauran alawuns da su ka karɓa bayan barinsu ofis zuwa asusun jihohinsu.

SERAP ta shigar da ƙarar Tinubun ne a ranar Juma’ar da ta gabata a Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos inda ta ke buƙatar kotun ta tilasta Tinubu wajen umartar tsofin gwamnonin kan su mayar tare da dena karɓar kuɗaɗen fansho da sauran abubuwan da ake ba su daga jihohinsu a matsayin ladan kasancewarsu tsofin gwamnoni.

SERAP ta bayyana cewar tilasta Bola Tinubu wajen sanya tsofin gwamnonin su aikata hakan a matsayin wani abu da zai temaki ƴan ƙasa musamman ganin irin halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi.

Lauyoyin SERAP, Kolawole Oluwadare da Andrew Nwankwo ne su ka shigar da ƙarar, yayin da kuma ake jiran kotun ta sanya ranar sauraron ƙarar.