Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

An Kama Mutane 7 A Yayin Da Zanga-Zangar Tsadar Man Fetur Ta Ɓarke A Kwara

Hukumar Tsaro ta NSCDC ta kama mutane bakwai da ake zargi da aikata ta’addanci a lokacin zanga-zangar ƙin jinin ƙarin farashin man fetur da direbobin haya suka yi a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.

Kakakin NSCDC na jihar, Ayoola Michael, ya ce waɗanda ake zargin suna cikin masu aikata ayyukan da suka saɓa doka da amfani da ƙarfi yayin zanga-zangar.

Ya ce, “A ranar Alhamis, 5 ga Satumba 2024, wata mai suna Olusegun Taiwo daga unguwar Sango, Ilorin, ta kai rahoton haɗa baki da satar kayanta ga ofishin NSCDC Jihar Kwara. Ta bayyana cewa, yayin da take hanyarta ta zuwa ofis, wasu matasa da ake zargin ƴan daba ne sun kai mata hari inda suka ƙwace jakarta, wayoyinta, da sauran kayayyaki masu daraja.”

Bayan samun rahoton, jami’an NSCDC sun kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata ayyukan da suka saɓa doka da tada zaune tsaye yayin zanga-zangar da direbobin Keke-Napep da babura suka gudanar a Ilorin a wannan rana.

Bayan gudanar da cikakken bincike, an gano cewa waɗanda aka kama suna cikin masu tada hankulan jama’a a Ilorin, musamman a unguwar Sango.