Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

An Yi Garkuwa Da Wasu Ƴan China 2 A Ogun

Wasu ƴan China su biyu masu suna Chen Wenguang da Liang Ding sun faɗa hannun masu garkuwa da mutane a yankin Kemta/Abule-Owu da ke kan titin Onigbedu a Jihar Ogun.

Jaridar PUNCH ta gano cewar, an yi garkuwa da mutanen ne a jiya Lahadi da misalin ƙarfe 1:45 da rana, lokacin da suke barin kamfanin da suke aiki don su kai wa abokansu ziyara.

Wata majiyar ƴansanda da ta nemi a ɓoye sunanta, ta bayyana cewar Wenguang da Ding fursunoni ne da ke aiki ƙarƙashin kulawar Kamfanin Good One Carton Company da ke yankin.

Majiyar ta ƙara da cewar Wenguang da Ding sun bar kamfanin ne a raɗin kansu ba tare da sun sanar da jami’an tsaro da ƴansanda da sojojin da ke tsaron kamfanin ko hukumar kamfanin ba.

Sai dai sun bayyanawa wasu abokan aikinsu cewar zasu je ƙauyen Kemta wanda bai fi nisan kilomita ɗaya daga kamfanin ba domin su ziyarci wasu abokansu.

Maimagana da yawun ƴansandan Jihar Ogun, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin, inda ta bayyana cewar, masu garkuwa da mutanen sun kira kamfanin suna neman kuɗin fansa kafin su saki ƴan ƙasar ta China, sai dai ba ta bayyana kuɗin da aka nema ba.