Wani abun tashin hankali ya ruɗa mutane jiya a birnin Ibadan, bayan da aka tsinci gawar wata matashiyar ma’aikaciyar jiyya mai suna Omoniyi Boluwatife.
Masu aikata aika-aikar, waɗanda har yanzu ba a kai ga gane su ba, sun yi wa Omoniyi kisan gilla ne, inda suka cire mata mahaifa.
Jaridar VANGUARD ta rawaito cewar, lamarin ya faru ne kwana biyu bayan ta yi rijista da Hukumar Kula da Ma’aikatan Jiyya da Ungozoma ta Najeriya.
KARANTA WANNAN: ‘Tana Kirana Ne Kaɗai Idan Tana Buƙatar Kuɗi,’ In Ji Wanda Yai Wa Budurwarsa Kisan Gilla
An gano cewar, Omoniyi wadda ta kammala karatun digirin a Lead City University, ta je wajen shaƙatawa ne wato club da daddare domin yin murnar samun rijistar da ta yi.
An ga wata mata da ke zaune cikin jami’ar Lead City tana kokawa kan irin kisan gillar da aka yi wa matashiyar.
Ta ce, sun faɗa musu cewar su na kulawa kan duk inda zasu je a daren, inda ta bayyana takaicin yanayin yanda rayuwar matashiyar ya zo ƙarshe.
Kafin daren da lamarin ya faru, an gano cewar, Omoniyi ta yi bankwana da mahaifiyarta wadda ta je har jami’ar daga birnin Port Harcourt domin taya ta murna.