Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ana Sama Da Fadi Da Ganga 500,000 Na Danyen Mai Zuwa Kasashen Waje

Kungiyar masu gidajen mai a Najeriya (PETROAN) ta bayyana damuwa kan yadda masu hakar danyen mai ke karkatar da ganga 500,000 na danyen mai da aka ware domin tacewa a Najeriya zuwa kasashen waje. 

Sakataren yada labarai na kungiyar, Joseph Obele, ya ce wannan matsala na hana matatun mai a kasar aiki yadda ya kamata, yana mai zargin kamfanonin hakar mai da fifita samun ribar dala fiye da samar da danyen mai ga matatun cikin gida.

PETROAN ta jinjinawa hukumar NUPRC bisa matakin da ta dauka na haramta fitar da danyen mai da aka ware don tacewa a cikin gida, inda suka ce hakan zai taimaka wajen bunkasa aikin tace mai a Najeriya.

“Muna da ganga 500,000 da aka ware don tacewa a cikin gida, amma galibi ana sayar da su a kasuwannin duniya,” in ji Obele.

Shugaban PETROAN na kasa, Billy Gillis-Harry, ya bukaci gaggawar aiwatar da dokar hana fitar da danyen mai domin tabbatar da cewa matatun cikin gida sun samu wadataccen mai. 

Hukumar NUPRC ta gargadi kamfanonin hakar mai da cewa duk wanda ya kasa bin ka’idojin samar da mai ga matatun cikin gida za a hana su izinin fitar da mai zuwa kasashen waje gaba daya.

Wannan mataki na daga cikin kokarin Najeriya na bunkasa karfin tace mai a cikin gida da rage dogaro da man fetur da ake shigo da shi daga waje.