A yayin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke cika shekaru biyu a mulki a wannan watan Mayun, jam’iyyar APC na ƙara ƙarfafa mulkinta yayin da manyan ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa ke cigaba da sauya sheƙa zuwa APC a shekarar 2025, matakin da ke iya sauya tasirin zaɓen 2027, kamar yadda ICIR ta tabbatar.
Rahoton ya nuna yadda gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na takarar Atiku Abubakar, Ifeanyi Okowa, suka jagoranci gaba-ɗayan PDP a jihar zuwa APC a ranar 23 ga Afrilu.
Haka nan Sanata Kawu Samaila daga Kano ta Kudu, Sanata Ned Nwoko daga Delta ta Arewa, da Shehu Sani daga Kaduna duk sun ajiye tutar jam’iyyunsu sun koma APC.
Baya ga hakan, dukkanin sanatoci uku na PDP daga Jihar Kebbi; Adamu Aliero, Yahaya Abdullahi da Garba Maidoki; sun bi sahu zuwa APC bayan sun gana da shugaban ƙasa a Villa.
WANI LABARIN: Shekaru 2 Bayan Ɗaukar Alƙawarin Tallafawa Ƴan Kasuwa, Tinubu Ya Ƙi Cika Alƙawari
A jihar Katsina, ƴan majalissar wakilai uku na PDP; Abubakar Aliyu, Yusuf Majigiri da Abdullahi Balarabe; sun sauya sheƙa zuwa APC a ranar 8 ga watan Mayu, inda suka danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar PDP.
Bayan haka, wasu ‘yan majalisa uku daga jam’iyyun NNPP da PDP; Kabiru Rurum daga Kano, Oluwole Oke daga Osun, da Sani Abdullahi daga Kano; sun bi sahu a ranar 15 ga watan Mayu.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa babu laifi idan Najeriya ta koma jam’iyya ɗaya idan hakan na wakiltar muradin jama’a.
“Jam’iyya ɗaya a ƙasa zaɓin al’umma ne… Idan sauran jam’iyyu sun ga tasirin mulkinmu suka yanke shawarar komawa APC, babu abin da ke da illa a ciki,” in ji Ganduje.
Sai dai masu sharhi na ganin cewa wannan sauya sheƙa na ruguza damar haɗewar jam’iyyun adawa domin kalubalantar APC a zaɓukan 2027.
ICIR ta bayyana cewa tafiyar APC yanzu na da ƙarfin da ke ƙara hana ƴan adawa fuskantar haɗaka ko ƙirƙirar sabbin dabaru na ƙarfafa kai.
Duk da haka, masu lura da siyasa na ganin cewa idan jam’iyya ɗaya ta mamaye ƙasa, to dimokuradiyya na fuskantar gagarumin haɗari.