Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

APC Ta Naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda A Matsayin Sabon Shugabanta Na Ƙasa

Jam’iyyar APC ta zaɓi Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa bayan murabus ɗin Abdullahi Ganduje saboda dalilan lafiya.

Yilwatda, wanda ke riƙe da muƙamin Ministan Harkokin Jin Ƙai, ya fito ne daga jihar Filato, kuma zaɓinsa yana cikin tsarin raba madafun iko na APC da ya bai wa yankin Arewa ta Tsakiya wannan kujera.

“Ya fi kowa, gogagge ne, kuma ba ya ɗauke da tarkon siyasar da zai hana jam’iyya samun ci gaba,” in ji wani babban jigo a jam’iyyar.

An cimma matsayar naɗa shi ne bayan taron da aka gudanar da daddare tsakanin shugaba Tinubu da gwamnonin APC a Abuja.

WANI LABARIN: Ƴan Jigawa Na Adawa Da Yunƙurin Gwamnati Na Gina Shaguna Kan Naira Biliyan 3.5 A Kano

Yilwatda, mai shekaru 56, ya kasance ɗan takarar gwamna a Filato a zaɓen 2023 amma ya sha kaye, sai dai an ba shi minista daga baya.

Ya taɓa zama malami a jami’ar Makurdi kuma ya yi aiki a matsayin kwamishinan zaɓe na INEC a jihohi biyar daga 2017 zuwa 2021.

“Zaɓensa yana nuna yunƙurin sabunta fuskar jam’iyyar da sake dawo da amincewar jama’a gare ta,” in ji wani daga cikin majalisar zartarwar jam’iyyar.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar sun bayyana cewa kasancewarsa Kirista zai taimaka wajen janyo hankalin mabiya addinai daban-daban.

Yanzu haka ana sa ran za a tabbatar da naɗinsa a taron NEC da ke gudana a yau, yayin da jam’iyyar ke fatan samun sabuwar hanya da sabuwar fuska gabanin zaɓen 2027.