Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

ASUU, ASUP, Bankuna Da Ma’aikatan Wutar Lantarki Sun Shiga Yajin Aiki Ƙarƙashin NLC

Ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, sun jaddada goyon bayansu na shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu da NLC ta fara a yau Talata.

Ƙungiyoyin sun haɗa da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU; Ƙungiyar Malaman Makarantun Kimiya da Fasaha, ASUP; ƙungiyoyin ma’aikatan da malamai na jami’o’i; Ƙungiyar Haɗin Kan Bankuna; da kuma Ma’aikatan Ɓangaren Inshora da Hukumomin Hada-hadar Kuɗaɗe, NUBIFIE.

Sauran sun haɗa Ƙungiyar Ma’aikatan Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa, NUATE da kuma Ƙungiyar Matuƙan Jiragen Sama da Injiniyoyin Jiragen Sama ta Ƙasa, NAAPE.

NUBIFIE da ke a matsayin ƙungiyar da ma’aikatan bankuna da na inshora ke ƙarƙashinta ta ce ta dakatar duk aiyukan ƴan ƙungiyarta a Najeriya.

Shugabancin NUBIFIE ya aika da sanarwa ga dukkan bankuna a Najeriya cewar, babu aiki a yau Talata 5 ga watan Satumba da kuma gobe Laraba 6 ga watan Satumba domin shiga yajin aikin gargaɗi da NLC ke jagoranta.

Su ma ƙungiyoyin NUATE da NAAPE sun tabbatar da cewar mambobinsu su shiga yajin aikin na duk faɗin ƙasa, a wata wasiƙa da suka aikewa rassansu da ke faɗin Najeriya.

Haka ita ma Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa, NUEE, ta umarci dukkanin mambobinta da ke faɗin Najeriya da su shiga yajin aikin na kwanaki biyu.

KARANTA WANNAN: NLC Ta Ƙi Yarda Da Kiran Gwamnatin Tarayya, Ta Jaddada Shiga Yajin Aiki

Mai Riƙon Babban Sakataren Ƙungiyar, Dominic Igwebike ne ya sanya hannu a sanarwar wadda ta bayyana cewar ma’aikatan lantarkin za su shiga yajin aikin ne don rashin jin daɗinsu da halin ƴan Najeriya ke ciki waɗanda su ka samo asali daga tsare-tsaren gwamnatoci.

Ita ma Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙungiyoyin Al’umma ta United Action Front of Civil Society ta umarci mambobinta da su yi zanga-zangar ƙin jinin matsatsin rayuwar da ake ciki a Najeriya.

A wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar, Wale Okunniyi ya sanya wa hannu ya ce, tallafin rage raɗaɗin cire tallafin mai wata hanya ce da ma su riƙe da madafun iko ke amfani da ita wajen ƙara kassara ƴan Najeriya.

Okinniyi ya ce, haɗakar ƙungiyoyin ci gaban al’umma sun yi watsi da waɗannan tsare-tsare na rashin kyautawa da Gwamnatin Tarayya ta gabatar waɗanda za su ƙara angaza miliyoyin ƴan Najeriya cikin ƙangin talauci.

Ya ƙara da cewar, a don haka, suna kira ga dukkan ƴan Najeriya su haɗa kai da NLC wajen buƙatar a janye tsare-tsaren da aka kawo waɗanda za su ƙara jefa talaka cikin ƙunci tare da kare kura-kuran gwamnati na gaza tafiyar da tallafin man fetur kamar yanda ta amsa laifinta a baya.