Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) ta yi gargaɗin cewa za ta sake tsunduma yajin aiki na ƙasa baki ɗaya idan gwamnati ta gaza magance matsalolin da suka daɗe suna addabarta da suka haɗa da rashin biyan haƙƙoƙi, lalacewar kayan aiki, da saɓa yarjejeniyar da aka sanya wa hannu.
Shugaban ASUU, Christopher Piwuna, ya zargi gwamnatin tarayya da na jihohi da watsi da alƙawuran da suka yi, yana mai cewa malamai “na jin an manta da su, an kunyata su kuma an raunana su” ta hannun gwamnatoci na baya da na yanzu.
Wannan barazanar ta biyo bayan iƙirarin Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, cewa “ba za a sake samun yajin aikin ASUU ko na jami’o’i ba har abada,” iƙirarin da ƙungiyar ta yi watsi da shi tana mai cewa “gwamnati ta daina magana ta koma aikata abu.”
ASUU ta bayyana mummunan yanayin rayuwa a jami’o’i inda malamai ke koyarwa “cikin yunwa,” ba sa iya biyan kuɗin wuta, kuɗin makarantar ƴaƴansu, ko samun kayan bincike kamar littattafai, sinadarai, da mujallu na zamani.
Piwuna ya zargi gwamnati da zaɓen abin da ta ga dama daga yarjejeniyar 2009 FGN-ASUU tare da maye gurbin tattaunawa ta gaskiya da “bayar da abu ɗan ƙalilan.”
Ya kuma soki shirye-shirye irin su “Diaspora Bridge,” yana mai cewa munafurci ne don kallon malamai a matsayin “masu sa kai” maimakon ƙwararru masu haƙƙin samun yanayi mai kyau na aiki.
Ƙungiyar ta nuna damuwa kan tsoma bakin siyasa a shugabancin jami’o’i, tana misalta matsalolin da suka biyo bayan naɗin Muƙaddashin Shugaban Jami’ar Alvan Ikoku mai cike da “rikice-rikice.”
Ta tunatar da gwamnati game da jerin yarjejeniyoyi tun daga 2013 da aka kasa aiwatarwa, tana mai gargaɗin cewa “babu wata yarjejeniya ko tattaunawa da za ta maye gurbin yarjejeniyar” da ke magance haƙƙoƙin ma’aikata da yanayin aikin bincike.
“Lokacin aiwatarwa yanzu ne,” in ji Piwuna, yana kira ga “dukkan ƴan kishin ƙasa na gaskiya” da su matsa wa shugabanni lamba kafin jami’o’in gwamnati su sake durƙushewa.