Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ba Mu Hana Ƴan Ƙasa Da Shekara 18 Rubuta WASSCE Da NECO Ba – Ministan Ilimi

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fayyace cewa ba ta dakatar da ɗaliban da ba su kai shekara 18 ba daga rubuta jarrabawar WASSCE ko NECO.

Ƙaramin Ministan Ilimi, Dr. Yusuf Sununu ne ya bayyana haka a Abuja yayin da yake amsa tambayoyi daga ƴan jarida a taron tunawa da Koyon Karatu da Rubutu ta Duniya ta 2024.

Sununu ya ce rashin fahimta da mummunar fassarar abin da Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya faɗa ya yi matuƙar baƙanta masa rai.

Ya bayyana cewa, Ministan yana magana ne akan shekarun shiga manyan makarantu na shekaru 18 kamar yadda ake aiwatar da tsarin ilimi na 6:3:3:4.

Ya ce, “Mun amince cewa za mu ɗauke shi a matsayin aikin da za a bi shi a sannu. Majalisar Tarayya tana aiki kuma mu ma muna aiki.”

Ya ƙara da cewa abin mamaki ne ganin cewa wata jami’a a ƙasar nan ta baiwa yara masu shekaru 10, 11 da 12 damar shiga jami’a, kuma wannan ba daidai ba ne.

“Ba mu ce ba za a sami wasu da suke ƙwari ba, muna sane cewa akwai waɗanda ke da basirar manya duk da suna da shekaru shida ko bakwai, amma waɗannan ƴan kaɗan ne.”

“Dole ne a sami doka, kuma ma’aikatar ilimi tana duba kafa tsarin gano yaran da suka ƙware, don kada iyaye su ce muna hana wa ƴaƴansu damar samun nasara.”

“Ba wanda ya ce babu yaro da zai rubuta WAEC, NECO ko wata jarrabawa sai idan ya cika shekara 18. Wannan kuskure ne da rashin fahimtar abin da muka faɗa,” inji shi.

Yayin da yake jawabi game da Ranar Koyon Karatu da Rubutu ta Duniya, Sununu ya jaddada muhimmancin koyon karatu wajen haɓaka fahimtar juna, zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.

Ya sake tabbatar da himmar Gwamnatin Tarayya wajen magance kalubalen koyon karatu ta hanyar shirin Education for Renewed Hope (2024-2027).