Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ba Za A Ƙara Siyen Kayan Waje A Najeriya Ba Sai In Babu Irinsa A Cikin Ƙasa – Gwamnatin Tarayya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabuwar manufar gwamnati mai suna Renewed Hope Nigeria First, wacce ke tilasta wa dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati fifita amfani da kayayyakin da ayyukan cikin gida, in ji Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, bayan zaman majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja.

Ministan ya bayyana cewa manufar za ta sa kowanne kobo da gwamnati ke kashewa ya koma wa ƴan Najeriya ta hanyar ƙarfafa masana’antu da rage dogaro da kayayyakin waje, inda ya ƙara da cewa za a fitar da umarnin shugaban ƙasa na musamman cikin ƴan kwanaki masu zuwa domin ba wa manufar ƙarfin doka.

“Daga yanzu babu dalilin da zai sa a shigo da kaya daga waje idan akwai irinsu a Najeriya,” in ji Ministan, wanda ya bayyana tsarin a matsayin makamancin dokar “America First” da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar.

WANI LABARIN: Nigeria Za Ta Jagoranci Ƙoƙarin Samar da Wutar Lantarki Ga Mutane Miliyan 300 A Afirka

Majalisar zartarwar ta umurci hukumar kula da sayen kayayyaki ta BPP da ta sake tsarin ƙa’idojin saye da kuma fitar da tsare-tsare don ƙarfafa kamfanonin cikin gida.

BPP za ta riƙa ƙididdigar kamfanonin Najeriya masu inganci da gwamnati ke yawan amfani da su, sannan za ta riƙa tura jami’an ciniki zuwa kowace ma’aikata.

Sabuwar doka ta haramta sayen duk wani kayan waje da ake da irinsa a cikin gida sai da rubutaccen izini daga BPP, sannan duk wata kwangila da ta danganci kayayyakin waje dole ne ta ƙunshi sharuɗɗan musayar fasaha, samar da kayan cikin gida, ko kuma horar da ma’aikata.

Gwamnatin ta kuma umurci dukkan ma’aikatu da su sake duba tsare-tsaren kasafin kuɗinsu na 2025 don daidaita su da sabuwar manufar nan take.